Tambuwal ya yabawa sojojin Nijeriya kan Martanin da suka kaiwa Mahara

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yabawa sojojin Nijeriya kan martanin da suka kaiwa Maharan ‘yan kungiyar ISWAP bayan sun kawo hari ga jami’an tsaron kasa a Sabon Birni, in da suka kashe jami'an tsaro 15 a sansaninsu dake ƙauyen Burƙusuma.

Tambuwal a bayanin da ya fitar wanda ya sanyawa hannu ya ce amadadin gwamnati da al’ummar Sakkwato muna jinjinawa sojojin Nijeriya kan jajircewa da sadaukarwarsu ga kawar da masu tayar da kayar bai a Nijeriya, za mu cigaba da ba ku goyon bayada rokon Allah ku samu nasarar kawar da wannan kalubale da kasar nan ke fuskanta.

Satin da ya gabata ne 'yan bindigar a wani harin bazata suka kawo a sansanin jami'an tsaro na haɗin guiwa.

Bayan tafiyarsu ne sojojin suka shirya suka bi su an bayanin da ba a tabbar ba.an ce an ceto soja biyar da aka kwato.