ADC ta mayar da martani kan zargin da Datti Baba-Ahmed ya yi mata
Jam’iyyar ADC ta mayar da martani ga kalaman da Datti Baba-Ahmed, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, ya yi kwanan nan, inda ta bayyana su a matsayin ra’ayinsa na kashin kansa.
A cikin wata hira da ya yi da tashar Channels, Baba-Ahmed ya ce haɗin kan adawa a ƙarƙashin ADC “yana yaudarar ’yan Najeriya”. Haka kuma ya bayyana aniyarsa ta sake yin takara tare da Peter Obi a babban zaben 2027.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, Jackie Wayas, mataimakiyar sakatariyar yaɗa labarai ta ƙasa ta ADC, ta ce kalaman Baba-Ahmed ba su wakilci matsayar jam’iyyar ko abokan haɗin gwiwarta ba.
“Sanata Datti Baba-Ahmed mutum ne mai daraja da ya dade yana tsaya wa gaskiya da rikon amana. Tun da haɗin kan nan ƙoƙari ne na bai ɗaya da ke buƙatar ƙarfafa da basirar dukkan ’yan kishin ƙasa, muna fatan zai shiga cikin tafiyar domin bayar da gudunmawa ga wannan hangen nesa na ceto Najeriya,” in ji sanarwar.
Wayas ta bayyana cewa an kafa haɗin kan ne bayan shawarwari da dama tsakanin manyan shugabanni irin su Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasa; Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna; David Mark, tsohon shugaban majalisar dattawa; Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan Osun; Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri; da kuma Peter Obi.
“Mai girma Mista Peter Obi ya bayyana a fili cewa ya kuduri aniyar yin aiki tare da haɗin kan, tare da rungumar ADC a matsayin dandali na babban zaben 2027,” in ji sanarwar.
managarciya