ƘADDARA TA: Fita Ta Tara
kasancewar mangariba ne yasa tayi raka'a shida idan Isha kuma raka'a goma sukeyi, sallama tayi ta tashi, taje bakin randa buɗewa tayi maimakon ruwa sai farin nono ne tas wanda babu datti ko kazanta, babban kwarya ta ɗauko ta zuba a ciki sannan ta ɗibi furan dake gefe tasa ta dama da cokalin duma sannan ta ɗau sugar ta zuba, ɗanawa tayi taji sanyi sosai, lumshe ido tayi tace "bari na kara madara sabida bako"
ƘADDARA TA: Fita Ta Tara
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 9*
~Kauyen da yake nesa dasu babban ruwan ne ya raba tsakaninsu da kauye ne sosai sabida babu abin more rayuwa ko kaɗan a ciki, wani kyakkyawan matashi ne yake sassake bishiya, sanye yake da kayan maharba fari ne dal asalin bafulatani ne, ya rataya takobi a bayanshi hankalinshi duk akan saran itacen da yake, wata kyakkyawar yarinya ce durkushe tana tsintan wasu ƴaƴan itacuwa da suka zubo, ɗaya ta ɗauka ta kai bakinta sanye take da riga da zani amma zanin guntu ne sosai, kanta babu ɗankwali gashinta an kumbutsa sau huɗu an ɗaure da igiya, jin karan faɗuwan abu a bayanta ta juyo subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangijin halittu, wani irin wutan kyau take dashi, fara ce dal tana kama da matashin sosai amma ta fishi hasken fata, murmushi tayi ganin katon mango ya faɗo da sauri taje ta ɗauka, kallon ruwan da yake gudu me yawa dake gabanta tayi, sai kuma ta kalli yayanta fuskanshi babu fara'a kuma da alama ya saba da hakan, cikin zazzaƙan muryanta tace "bari naje na wanke"
tafiya tayi da duka kayan itatuwan a hanunta taje bakin ruwan ta zauna ta aje a kasa, fara ɗauka tayi tana wankewa da ɗaɗɗaya, sa ɗaya tayi a karamin bakinta ta fara tsotsa zaƙi zaƙi tsami tsami abin yake dashi, tashi tayi tace "bari na wanke jikina dama nayi datti"
sa kafanta tayi cikin iya ruwan ta fara shiga ciki sosai, kafanta ta wanke sannan ta wanke hanunta, nishaɗi take yi sabida sai dariya take tana wasa da ruwan, cire kafanta tayi zata fita taji kamar ta taka abu kuma ba dutse ba, da sauri ta kara kallon ruwan sannan ta kara takawa, hanu tasa tana taɓa abin, jin kamar mutum ne jikinta ya fara rawa, a tsorace ta durkusa ta ɗaga, waro ido tayi ta buɗe murya hanunta rike mutum data tsinta a ruwan tace "HAMMA NAJEEB? kazo na tsinci mutum"
aje addan da yake sara dashi yayi sannan ya kalleta yayi tsammanin haukan data sama ne zatayi mishi, baiyi magana ba yazo inda take, niyanshi idan karya tayi saiya sassauke mata mari, yana zuwa ya kalleta yaga da gaske tana rike da abu, waro ido yayi ganin mutum ne an ɗaure baki da hanci, goshinta ya farfashe ga kuma jikinta daya farfashe sabida duwatsun dake cikin ruwa wanda tayi ta karo dasu, da sauri ya shigo ya ɗagata ya cirota daga ruwan, a kasa ya kwantar da ita yana kallonta, tace "hamma najeeb baya raye ko? ya mutu?"
taɓa hanunta yayi sannan ya girgiza kai yace "yana raye bai mutu ba"
cikin gurɓataccen hausanshi da yafi nata muni yayi maganan, kwanceta yayi sannan yace "kawo ganyen kalgo"
da gudu taje inda yake saran itacen ta ɗauko wani ganye a kwarya tazo dashi, yace "daddaka"
dakawa tayi tasa a kwaryan yace "sa ruwa"
hanunta tasa ta ɗibo ruwa kaɗan ta zuba sannan ta juya sosai da hanunta ta kawo mishi, yace "zauna"
zama tayi, yace "shafa mishi a wuya da goshi da kai"
shafa mata tayi sosai yace "kara ruwa ki bashi yasha"
kara ruwa tayi sannan tazo ta ɗaga kanta ta ɗaura a cinyarta ta fara bata ruwan ganyen, tari ta fara amma bata buɗe ido ba, ta kalleshi yace "cigaba da bashi"
tace "to"
cigaba tayi da bata, shi kuma ya riko hanunta yana shafa hanunshi sosai a nata, ya saki hanun ya rike kafan yana shafawa sosai yana kallonta har yanzu idonta a rufe, sun ɗau lokaci a haka kafin yace "kwantar dashi ki kawomin itacen dana sara"
kwantar da ita tayi ta ɗauko itacen da yake ɗanye ta bashi, ɓare bayan yayi ya murza a hanunshi sannan ya shafa mata a fuska yace "rike kafanshi sosai"
rike kafanta tayi, shi kuma ya rike kanta yasa baki a kunnenta ya fara wani irin karatu yana murza tafin hanunta da karfi, buɗe ido tayi a firgice ta kalleshi, fuskanshi babu alaman wasa ya saketa, dariyan farin ciki yarinyar tayi tace "hamma najeeb ta tashi wallahi"
ya tashi yace "rikeshi mu tafi gida"
tace "to"
kallon meenat dake binsu da kallo tayi tace "tashi muje gida idan ka huta saika koma garinku"
a hankali ta tashi, rike hanunta tayi shi kuma ya kwashe itacen duk yawan itace da nauyinsu bai nuna gajiya ko kaɗan ba sai tafiya yake yana gaba suna biye dashi, tafiya me nisa sukayi kafin suka shiga kauyensu mutane ta gani suna kallonta ga mutanen garin kamar mayu, tsoro ne ya kamata yarinyar tace "kar kaji tsoro babu abinda zai sameka hamma najeeb ba zai bari ayi maka komai ba"
binta kawai take da kallo, tanada tabbacin wannan mayu ne domin daga suturan jikinsu da kuma dattin dake jikinsu da fatarsu da idanuwansu da suka nuna tsantsan rashin imani dake tare dasu, hanunta gam ta rike na yarinyar dashi, da haka har suka isa wani gidan taɓo me ɗaki kanana biyu, shiga sukayi wata kyakkyawar karamar yarinya tazo da gudu ta rungume yarinyar tace "kun dawo Adda"
ta gyaɗa kai alaman eh, ta kalli meenat tace "waye wannan adda?"
tace "bako ne mukayi"
tace "sannu bako"
a hankali ta gyaɗa kai tana kallon yarinyar wacce tayi kyau cikin kayan fata brown, skin nata kamar bana mutanen kauye ba, shimfiɗa mata tabarma tayi tace "ka zauna anan"
zama tayi tana bin ko ina da kallo harda shi hamma da yake dama wani abu a kwarya, suma suka zauna a gefenta tace "yaya sunanka?"
nuna kanta tayi, tace "ni?"
gyaɗa kai tayi tace "eh kai"
ta girgiza kai tace "nima ban san sunana ba na manta sunana"
kanta ta rike tana jin yana sarawa sosai, da sauri ta riketa tace "sannu"
kwanciya tayi a wajen tace "kaina yana ciwo sosai"
tsaye yayi a kansu ya bata maganin daya dama a kwaryan yace "ka bashi ya kara sha ka shafa mishi a jiki"
ɗagata tayi tace "tashi kasha"
tashi tayi tana rufe ido tasha, shafa mata sauran tayi a jiki, take bacci ya ɗauketa ta kwanta a wajen, tagumi yarinyar tayi tana kallonta tace "Allah sarki ya manta komai watakila faɗuwa yayi a ruwa"
yana alwala yace "wurgar dashi akayi ba faɗuwa yayi ba"
daga nan bai kara cewa komai ba ya fice daga gidan.
tana zaune cikin tausayinta sannan ta tashi ta ɗau buta tayi alwala kusan sau biyar biyar take wanke duk inda ake wankewa sau uku idan za'ayi alwala, wani fata ta ɗauka ta shimfiɗa sannan ta ɗau karamin ɗankwali ta yafa ta fara salla, kasancewar mangariba ne yasa tayi raka'a shida idan Isha kuma raka'a goma sukeyi, sallama tayi ta tashi, taje bakin randa buɗewa tayi maimakon ruwa sai farin nono ne tas wanda babu datti ko kazanta, babban kwarya ta ɗauko ta zuba a ciki sannan ta ɗibi furan dake gefe tasa ta dama da cokalin duma sannan ta ɗau sugar ta zuba, ɗanawa tayi taji sanyi sosai, lumshe ido tayi tace "bari na kara madara sabida bako"
madara ta kara sannan ta kara sugar yayi daɗi sosai ta rufe, saida tayi sallan Isha kafin taga hamma ya shigo hanunshi rike da leda, da sauri taje ta karɓa, zama yayi a inda ya saba zama zuba mishi nonon tayi a karamin kwarya tasa mishi cokali ta kawo mishi, ledan da yazo dashi ta buɗe taga nama gasashe me zafi cike da ledan taje ta ɗauko kwano ta zuba mishi dayawa ta kawo mishi, meenat ce ta fara motsa hanu, a hankali ta buɗe ido taji kanta ya daina ciwon sai ciwon jiki da takeji kaɗan kaɗan tashi zatayi yarinyar tazo da sauri ta ɗagata, zama tayi ta kalleshi baya kallonsu nonon kawai yake sha, ta kalli yarinyar tace "ina nake? nan inane?"
kawo mata nonon tayi tace "kisha sai nayi miki bayani"
sha tayi sosai sannan tace "nasha to ki faɗamin nan inane?"
tace "sunan kauyennan tudum mu ba mugaye bane mu fulani ne masu kiwo da kuma bada magani a ruwa muka tsinceki nida hamma na"
tace "to daga ina nake? me yasani a ruwa?"
girgiza kai tayi tace "wannan tambayan ke zamu yiwa sabida bamu san daga ina kike ba"
tace "bazan iya tuna komai ba"
karamar yarinyar tace "abani naman da kawu ya kawo"
bata naman tayi ta fara ci, tayi shiru tana kallonsu tace "ya sunanta?"
nuna yarinyar tayi tace "wannan?"
gyaɗa kai tayi, tace "sunanshi MIMI"
da mamaki tace "ke kuma fa?"
nuna kanta tayi tace "ni?"
tace "eh"
tace "sunana ASMEETA amma ana kirana Asmee"
da mamaki a wannan kauyen amma suka san irin waɗannan sunayen tace "Asmee?
tace "eh ke kuma me sunanki?"
girgiza kai tayi tace "ban san sunana ba"
murmushi tayi ganin tana damuwa ta riko hanunta tace "karka damu zamu rinƙa ce maka AMEENA"
maimaita sunan tayi "Ameena?"
gyaɗa kai tayi tace "yayi daɗi ai ko?"
tace "me yasa zaku kirani da Ameena?"
tace "sabida sunan mamana ne amina kuma ta mutu"
shiru tayi tana kallonta yadda take share hawaye da alama tana jin zafin maganan.
tace "wannan kanwarki ce?"
tace "a,a ƴata ne"
shiru tayi tana kallon ysrinyar, saida duhu yayi sosai kafin suka shiga ɗakin da yake da matsi sosai sai tarin magani da alama suna bada magani sosai.
Aneeta bacci take cikin kwanciyar hankali, hameed ne ya fara tashi kallonta yayi sai kuma ya sauka ya shiga bathroom yayi wanka tareda alwala ya fito yasa jallabiya me kyau salla yayi sannan ya zauna akan sallayan yana addu'a a cikin ranshi, a hankali ta fara buɗe ido sauke idon tayi a kanshi sai kuma ta rufe ido, a hankali ta sauka daga gadon ta shiga toilet tayi wanka tareda alwala ta fito, cire towel ɗin tayi ta ɗauko simple dogon riga tasa, sallayan da yayi sallan tayi salla akai, juyowa tayi cikin respect ta gaisheshi, a hankali ya mika mata hanu suka gaisa, murmushi tayi tace "bari naje na gaida su ammi"
tashi yayi suka fita tare, ɗakin ammi taje ta buɗe kofan ta tsaya a bakin kofa babu sallama, Ammi wacce yanzu kenan fitowanta daga bathroom baya tayi da dafa kirji tace "Innalillahi"
tsirata tayi da ganin Aneeta, murmushi tayi tace "ammi tsoro na baki?"
shiru tayi tana kallonta, tazo ta zauna a bakin gadon tace "kar kiji tsoro Ammi niba abin tsoro bace"
ammi tace "meya shigo dake?"
tace "gaisuwa"
yadda take amsawa a tsaye yasa take jin wani iri a kanta, tace "to tashi ki fita na amsa"
make kafaɗa tayi tace "um um babu inda zanje tare dake zamu fita"
tace "tashi ki fita aneeta"
tace "meyasa kike koran sirikarki? ko dai haka kike kore kowace sirikarki ne?"
ammi ranta ya gama ɓaci tace "ni kike gayawa wannan maganan aneeta?"
tashi tayi tana nufota, baya ammi ta fara a tsorace, saida ta isa jikin bango ta tsaya tana kallon Aneeta a mugun tsorace, ɓata rai tayi ta zama asalin aneeta tace "haka kike koran zeenat?"
a razane ammi ta kalleta, ya akayi ta san zeenat? shine tambayan da takeyi a zuciyarta, murmushin gefen baki tayi tace "karki damu ni ba zaku kasheni kamar yadda kuka kashe zeenat ba"
fita tayi daga ɗakin, da razanannen kallo Ammi tabi bayanta, banda rawa babu abinda jikinta yake, idanu a waje tace "waya bata labarin? hameed?"
da sauri ta girgiza kai tace "no hameed ba zai taɓa bada wannan labarin ba, kaseem? no kaseem ba zai bata ba to waye? meenat?"
da sauri tace "meenat"
fita tayi daga ɗakin a tsorace ta shiga ɗakin meenat bayan tayi knocking sosai bata buɗe ba, tana shiga tace "meenat"
gani tayi babu ita akan gado, tayi knocking toilet taga ya buɗe alaman babu kowa a ciki, fita tayi daga ɗakin tana kwala mata kira "meenat? meenat?"
sultan daya shirya domin zuwa school ɗin da Abi ya sashi yace "ammi ina meenat ɗin ban ganta ba nima tun ɗazu nake nemanta"
tace "to ina taje sultan?"
yace "wallahi ban sani ba har fada na dubata ban sameta ba"
ammi tace "ka sanarwa kowa a fara nemanta"
yace "to"
sanarwa sukayi take aka fars nemanta a gidan babu ita, ammi cikin tashin hankali tace "na shiga uku na lalace ina ta shiga?"
kaseem wanda zufa ya wanke mishi fuska share zufan yayi yace "Innalillahi me yake faruwa a wannan gidan?"
kamar da wasa sama da kasa aka nemi meenat aka rasa, har gidan rediyo da gidajen tv an dubata babu ita, ammi hanu ta ɗaura aka ta kwala wani uban ihu tace "meenat kar kimin haka"
kaseem jiri yakeji zama yayi akan sofa, sultan kuka ya fara, hameed kuma yana tsaye cikin tashin hankali, ammi idonta ne ya sauka akan Aneeta wacce itama kallonta take, cikin hawaye da zafin rai tace "ina zargin Aneeta da ɓatan meenat"
duk suka kalleta a razane jin abinda ta faɗa, tace "wallahi Aneeta tanada sa hanu a ɓatan meenat"
kaseem cikin gajiya da lamarin gidan yace "kada ki kara maimaita wani kuskuren"
tace "babu kuskuren da na aikata ban yadda da ita ba"
aneeta kallonta take tana hawaye, hameed dafa kanshi yayi idonshi a rufe ya rasa me ma zai fara yi.
Ammi tace "ina ƴata?"
Aneeta tace "wa..wa..wallahi ban san komai ba..."
da mari ta ɗauketa tace "ina ƴata nace?"
tana girgiza kai a tsorace taje bayan hameed ta tsaya tace "wallahi ban san komai akan ɓatan meenat ba"
zata kara marinta kaseem yace "ammi kada ki kara taɓata domin batada laifi, yadda kika yiwa zeenat kikeso kiyi mata?"
toshe kunne haneed yayi, tace "kaseem ai zeenat kafi kowa sanin waya kasheta, kasan kaine babban abin zargi tunda kaine...."
cikin wani irin rawa da jikinshi yake na ɓacin rai yace "kece abin zargi bani ba ke ai kin san kece kika kasheta sabida kisa rayuwan hameed a masifa"
sultan ganin kamar zasu daki juna yace "dan Allah ku daina tuna abinda ya wuce ku daina"
yace "ka barni na faɗi komai ka bari a tona komai, yau saina tona kowa ma ya sani, matar hameed zeenat kowa yasan ammi ce ta kasheta..."
Ammi tayi dariya wanda yafi kuka ciwo tace "me zaisa na kashe zeenat tana matsayin matar ɗanal? kai de kaida kake da kyakkyawan alaka da ita kaine ka kasheta sabida kada ta tona asirinka idan kuma ba kai ka kasheta ba to ko kaffara ba zanyi ba hameed ne ya kasheta...."
centre table ɗin dake gabanshi yayi watsi da kayan dake kai yace "dani da hameed kike zargi?"
tace "ba zargi bane na tabbatar kaseem"
ya nuna hanunshi zuwa kofa yace "saide ke da hakeem ai kinfi kowa sanin menene tsakaninta da hakeem sabida kada ta fada kika kasheta, na rantse da Allah dake da hakeem a cikin biyu ku kuka kasheta kuma hakeem shine wanda ya kasheta domin a hanunshi akaga...."
wani tsawan da ammi ta daka a wajen saida duk suka tsorata tace "babu abinda zai haɗa hakeem da matar ɗan uwanshi..."
yace "shiyasa kullum yake zuwa ɗakinta da dare? me yake zuwa yi?"
tace "kai me ya kaika har kasan tana zuwa?"
sultan idonshi akan Aneeta wacce take murmushi kasa kasa da alama wannan sirrin take son ji, hanunta ya rike kara tayi tace "ka sakeni sultan"
kaseem yace "ka saketa sultan"
bai kallesu ba kawai ya fara janta har stair, wurgar da ita yayi bayan ya shiga ɗakin ya rufe kofan yace "ina meenat?"
tace "wallahi sultan ban san komai ba"
yana nufota yace "ina meenat?"
baya ta fara daga zaunne tana girgiza mishi kai tana hawaye tace "wallahi ban sani ba"
mari zaiyi mata ta rike hanunshi gam, tashi tayi tana kallon cikin idonshi tace "me kake tsammani sultan kanin mijina? nice zaka mara? hmm tunda kanason jin komai bari na faɗa maka meenat na kasheta kuma na bawa kifaye gawanta su cinye, kasan meyasa?"
dariya tayi kaɗan tace "sabida sunana Aneeta lawan lamba"
a razane yake kallonta bakinshi yana rawa yace "m...m..me?"
ta saki hanunshi ta juya baya tace "eh sunana kenan na gaskiya"
yace "kenan ke kanwar zeenat ce?"
juyowa tayi tana smiling face "unty zeenat ko kuma zeenat haka gatsau? Anyway ni kanwar zeenat ce wacce kuka kashe a ranan data haihu ba ita kaɗai ba har jaririn data haifa saida aka salwantar, kuka bata wahala kamar baiwa, kuka sa ta tsani rayuwa da abinda ke cikin duniya baki ɗaya, kuka azabtar da ita har saida ta haukace sabida azaba daga karshe kukayi ajalinta, na rantse banzo gidannan ba saida na shirya, dukanku saina ɗau fansan abinda kuka yiwa yayata, daga ni sai ita mahaifiyarmu ta haifa na taso cikin kaunar yayata zeenat, batada masoyiya saini"
share hawaye tayi tace "dani da zeenat wannan auren shine ya fara raba duk wani shaƙuwan da mukayi, yayanku hameed shine mugun daya fara lalata mata rayuwa yasa mata ɗaci a ranta, yasa ta rasa hope, daga karshe ya kasheta"
kallonshi tayi tace "jeka ka faɗawa kowa cewar ni kanwar zeenat ce, jeka"
a hankali ya fara yin baya yana kallonta, hanu yasa akan kofa zai fita tace "sultan"
tsayawa yayi, tace "idan kaje faɗa musu kada ka manta ka faɗa musu kana canja alluran da ake yiwa hameed"
a razane ya cire hanunshi dake jikin handle yana kallonta idanunshi kamar zasu zubo, tayi murmushi me sauti tace "ka fasa zuwa ne? kaje mana sultan allura kawai kake canjawa idan ka faɗa musu ba zasu maka komai ba"
ganin ya tsaya turus ta fara takawa a hankali tasa hanu akan handle ɗin tace "tunda ba zaka faɗa musu ba ni bari naje na faɗa musu"
hanunta ya rike yana girgiza kai, murmushi ta kumayi tace "sakeni mana sultan"
bakinshi yana rawa yace "ki rufamin asiri ya kaseem zai kasheni"
tace "zan rufa maka amma akan sharaɗi"
ganin ya kasa magana tace "ko da wasa kada bakinka yayi kuskuren faɗawa kowa abinda ya faru, sannan duk abinda zanyi ya zama dole ka tayani ko kanaso ko baka so har sai na cimma burina a gidanku"
tace "ka amince?"
a hankali ya gyaɗa kai, tace "deal"
fita tayi daga ɗakin ta gansu tsaye hameed kuma yana zaune dafe da kanshi.
_Jiddah ce...
08144818849
managarciya