HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Ban Al'ajabi Da Rikitarwa, Fita Na 31

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Ban Al'ajabi Da Rikitarwa, Fita Na 31
HAƊIN ALLAH: 
 
   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 
 
 
Page 31
 
 
Cak ta tsaya tana kallonsa, domin jin dalilin kiranta da ya yi, har kira biyu.
 
Rasa abin da zai ce mata ya yi domin baki ɗaya sai yaga tai mai kwarjini bakinsa ya fasa furta gaskiyar abin da ke ƙasan ransa, don haka sai ya ce mata, "Ki kira wayarta mana ki ji ko tana ina tunda bata nan gidan."
 
Kamar haɗin baki tsaki kowace ta ja ta koma inda take zaune tana taɓe bakinta.
 
Jiddah ta ɗan yi murmushin da bai barin fuskarta tace, "Tunanin da ban yi ba kenan, ko da yake ban ma fito da wayar ba, amma bari na koma sai na je na kira ta a wayar."
 
 
Ba tare da ya kasa ɗauke ido daga fuskarta ba ya ce, "Bari na kira maki ita mu ji ko tana kusa, ya saka baki ya kwaɗa wa Maryam kira domin ita ce ƙawarta. Yi tai kamar bata ji shi ba sai da ya kira ta kusan sau huɗu sannan ta ɗaga labulen ɗakinta tana yamutsa fuska tace, "Lafiya kake ta kirana kamar mai bina bashi?"
 
 Shi ma dai cikin fuskar rashin walwala ya ce mata, "Number ƙawarta Bilkisu za ki ba da a kira wa wannan taji ko tana ina."
 
 Kamar ba zata ba da ba, don bata ce komai ba, ta koma saki labulanta ta koma ɗaki.
 
Jiddah har ta saduda zata tafi sai kawai ta ji muryar Maryam ɗin na karanta ma Mustapha number don haka ta saurara kaɗan.
 
          Ta sowa ya yi har gabanta, yana kiran wayar har ta ɗaga ya gaya mata Jiddah ce ke neman ta gata nan gidansa. 
 
Bayan ya kashe wayar ya dube ta fuska fal farin ciki ya ce, "Kin ji ta koma gidanma yanzu haka wai daman markaɗen kayan miya ta amso."
 
 Jiddah cikin murmushinta tace, "Na gode bari na je to." Ta juya ta fice ya bita da kallo har ta rufe ƙofar gidan idonsa na kan ƙofar.
 
Maryam dake kallon komai ta tagar ɗakinta ta ja tsaki tace, "Sai shegen son matan tsiya ba kirki. Wa ya sani ma ko jawararsa ce? Aikin banza."
 
Jiddah na shiga gidan Bilkisu ta ja ajiyar zuciya tace, "Kai Yau naga ikon Allah! Su kuma haka tsarin su yake ? Tabdijam kowa dai da halinsa."
 
Bilkisu tai dariya don tasan an yi wani abin ne gaban idonta tun da lambar maigidan ce ya kira ta da ita to ba shakka tasan cewa an tabka wani abin gabanta wanda gidan ne kawai ake irinsa a unguwar.
 
"Hala faɗa su kai sababbun?" Cewar Bilkisu tana dariya.
 
"Uhmm! Ban iske ko ɗaya ba a tsakar gidan sai maigidan da yaran kawai yadda naga gidan ne bai min ba, shi kanshi maigidan a dame yake ko mai yasa oho!
 
Dariya Bilkisu ta sake kashewa da ita tace, "Ai wallahi kaɗan ki ka gani indai gidan Mustapha ne, bawan Allah yana amsar wuta gidan nan ai, ko da yake ai maganin masu auren mata barkatai kenan, ka tara yara ka tara mata ai ta fitina kullum cikin rabon faɗa kake, ko da yaushe cikin tashin hankali kake na rashin  zaman lafiyar gidanka. Amma wallahi yana ban tausai domin yana bakin ƙoƙarinsa kawai dace ne bai yi ba, a zahiri kowa ɗauka yake laifinsa ne matsalar gidansa amma mu da muke tare da su mun san cewa laifin matan ne."
 
"Ke ji mata sai wani kare shi kike, nifa duk abin da aka ce namiji zai yi wallahi ban cewa bai iyawa, komai aka ce namiji na yi wa mace yadda nake da gudun gaske ma, domin maza basu da tabbas ko da wasa namiji bai tausan mace yadda take tausansa, ke a takaice ma dai Ni nan da kike gani babu abun da na tsana irin aure da soyayya."
 
Bilkinsu ta dubi Jiddah sosai tace, "Ƙawata bari ki ji na gaya maki gaskiyar magana, Mustapha ɗan gayu ne, ga tsabta sannan irin mazan nan ne masu son rayuwar kulawa da nuna soyayya sai dai bai dace da samun irin haka ba daga kowace daga cikin matan nasa. Amma wallahi nasan da zai samu wadda zata kula da shi ta tarairaye shi tayi mai duk abin da yake so wallahi sai an yi mamakin yadda zata rayu da Mustapha cikin farin ciki Jiddah, domin nasan Mustapha yafi mijina kyawawan halaye nesa ba kusa ba wallahi har addu'a nake Allah Yasa nawa mijin ya koyi irin halayen Mustapha."
 
Jiddah ta taɓe bakinta tace, "Ke Ni ba gulmar wani gida ta kawo Ni ba, zuwa nayi na ji idan an kawo kayan yaran da kika ce na saidawa na gani idan akwai daidai na yarana amma kin tasani da maganar wani can da ba ruwana da shi."
 
 
Bilkisu tace, "Ke fa ƙawata na lura Deeni ya cire maki duk wani so da yardar maza a ranki, kuma ba haka bane ba akwai tarin maza masu kula da tarairaya irin wadda kowace mace ke mafarkin samu a gidanta."
 
"Allah Ya kyauta! Ni da aure sai idan ana yi a lahira na yi amma a duniyar nan ban ce na rantse ba amma kam babu Ni babu wani aure Bilkisu."
 
Babu yadda Bilkisu ba tai ba, amma Jiddah ta kasa fahimtar ta, don haka suka bar maganar suka koma kan kayan da za a kawo na yara Jiddah zata siya."
 
  Tunda ta fice daga gidan ya koma ɗakinsa yana jin wani abu na yi mai yawo a cikin jikinsa da zuciyarsa. "Wane irin so ne wannan mai ƙarfi ke yawo a cikin jikina na yarinyar ne? Wace irin soyayya ce wannan nake mata? Na tsani auren amma gani da kaina nake hasaso rayuwar aurena da yarinyar me hakan ke nufi?"
 
Ya sake zuyawa yana ajiyar zuciya ya ce a bayyane, "Ina cikin matuƙar damuwa amma kuma nake jin ki a raina, cike nake da damuwa amma nake jin ke ce za ki cire min damuwar, na kasa natsuwa domin ban da ita amma dana ganki sai na manta tashin hankalina, don Allah Jiddah ki tausaya wa rayuwata ki zama cikon mafarkina kamar yadda nake gani a mafarkina na aureki muna rayuwa mai cike da tsabta da farin ciki muna rayuwa tamkar ko da yaushe sauyo mu ake saboda rashin damuwa.
 
Idan bai manta ba, Salim na yawan gaya mai cewa, ya ƙara haƙuri akwai lokacin da komai zai wuce a wajensa kamar yadda zai wuce a wajen Jiddah, bai taɓa tambayar wane irin hali yarinyar take ba, har Salim ya rasu, domin a tunaninsa ba huruminsa bane ba tunda gidan wani take, amma a yanzu ji yake so yake ya ji wane irin hali ne wanda yarinyar tai a gidan aurenta? Amma gun wa zai ji? Hajjo ce amma ya zai ya tunkari Hajjo da maganar?
 
Yana cikin halin da ya kamata ya tarkata babin mata ya rufe a rayuwarsa hakan shi ne daidai amma me yasa Jiddah ke kai da kawowa a ransa da zuciyarsa? 
 
Tana matuƙar birgeshi yarinyar ko da yaushe cikin fara'a take, baka taɓa ganinta da fuskar damuwa alamar tana tare da godiyar Ubangiji kenan tunda tana da yakana a tattare da ita.
 
 
Asma'u ce ta faɗo ɗakin ba sallama ta wurga mai harara da jakar kayanta a hannu tace, "Na lura komai na gidan nan nice a banza ce nice wadda bata da ƴancin kanta balle na ƴaƴanta don haka zan koma gidanmu na gaji da wannan baƙin zaman mai cike da takaici da mugun son kai."
 
 
Mustapha ya dube ta ya kasa tanka mata, domin mafi yawan lokuta idan suna mai irin wannan shirmen kasa magana yake su kuma sai su ɗauki hakan matsayin wulaƙanci ne da son kai daga gare shi.
 
Ta sake ɗaga murya sosai tace, "Daman ai nasan ba zaka tanka ba, tunda ba nice nace ma matarka na satar abinci tana saidawa da kaiwa gidansu ba."
 
Sai a lokacin ya buɗe baki cikin takaici ya ce,"Ke wai wanda ku kai bai ishe ki bane sai kin biyo nan kin sake min wata fitinar ne? Wai me yasa baki san zaman lafiya ne? Wuce ki ban waje kada ki sake ɓata min rai, ba dai abin da kika ga yayi maki ba kenan, to ki je kiyi ta yi." Ya juya ya gyara kwanciyarsa ya lumshe idonsa kamar mai barci.
 
Tai ta ƙananan maganganun ta son ranta tana kiran shi azzalumi mugu da bai san adalci ba, shi dai bai sake tanka mata ba, kamar yadda ba zai hanata zuwa gidansu idan yajin nata ya motsa ba.
 
Maryam kuwa sai abin ya yi mata ciwo ganin Fatima ta shige ɗakin Mustapha ta yi shiru kuma bata jiyo hayaniyar su sai ta ɗauka ya sata ɗaki ne yana lallashinta ita kuma ko oho tunda ba ƙaunarta yake ba yanzu. Sai zuciyarta ta dinga tafasa har tana jin ma ta je ɗakin ta haɗa su duka ta ci masu mutunci kawai ko zata ji sauƙin zuciyarta dake ƙuna.
 
Tana tsaye gun tagar ɗakinta ta ga Fatimar ta fito fuskarta ba wata damuwa ta shige ɗakinta, bayan da farko tasan yaji ne tai niyyar yi, amma da yake munafuki ne shi ne ya lallashe ta waya sani ma ko har zagina ya yi gabanta don ya faranta mata rai?" Ai sai ta kwasa ita ma cike da fushi ta nufi ɗakinsa, kamar dai yadda suka saba ba sallama ta ambaci sunansa kai tsaye cike da rashin kunya tace, "Mustapha ka ji tsoron Allah wallahi ba zan taɓa yafe munafurta ta da kake ba da zalunta ta ba a cikin gidan ba, sai Allah Ya saka mun wallahi."
 
Kallonta yake ita ma kamar Fatimar, ba wata kwalliya balle ƙamshi kayan jikinta duk sun yi datti kamar wata tsohuwa haka take cikin kayan ba mai cewa yarinyar mace ce ita.
 
Wani takaici ya sake kama shi, sam bai dace ba ta kowane ɓangare, yana son yaga mace cikin kwalliya yaga mace nata ƙamshi uwa uba ya ganta cikin ƙananan kaya amma shi duk babu abin da matansa ke da ra'ayin yi daga ciki, idan ya yi magana suka saka ƙananan kayanma da ya shiga sashensu sai su dinga ɓoyewa suna kakkarewa abin sai ya ba shi haushi kawai ya fice.
 
Kallo guda ya sake bin ta da shi ya gyara kwanciyarsa, alamar bai da lokacinta.
 
Ta fasa kuka ta zauna daɓas tana cewa, "Ai daman nasan ba zaka kula Ni ba tunda baka sona yanzu to wallahi nima yanzu haka ne kar kai tunanin akwai sauran ragi da ragowa a tsakaninmu."
 
Tamkar zubar dalma kan rauni haka yake jin kalamanta, bai san yaushe za su gane gaskiya ba, bai san yaushe za su gyara halayensu ba, ji yake kaf duniyar yafi kowa damuwa indai maganar iyali ne.
 
Yanzu yana sakinsu za a cigaba da saka shi bakin duniya kamar yadda yake ciki daman, mutane ba su yi mai uzuri ba su san gaskiyar komai ba amma shi suke cewa bai da halin kirki baki ɗaya cewa ake bai iya riƙon aure, babu irin maganganun da basu dawowa kunnenshi da ake yi na bai da kirki matansa wahala suke sha.
 
Bai san lokacin da hawaye suka zubo mai ba, ya cigaba da hasaso muggan maganganun da ake yi kansa, duk dai akan matan nasa.
 
An manta da cewa duk baƙin halinsa da ace ya samu mace guda wadda zatai rayuwar aminci da mutunci da shi tabbas da kowa sai ya yi sha'awar gidansa.
An manta da cewar mutum guda bai iya tafiyar da rayuwar farin ciki a zaman aure dole dai da taimakon abokin zamansa.
An manta cewa shi namiji ne aiki yake zuwa fafutuka yake dare da rana don kawai ya ji daɗin rayuwarsa gidansa, domin da bai da iyalin wasu lamurran duk ba zai yi su ba amma a banza.
Mutane sun manta cewa shi ne ya aje matan don haka shi ne ya kamata ace matan na bi suna yiwa ladabi da biyayya suna jin tausansa suna yi ma shi uzuri kan duk wasu ƙananan lamurran da suka shafi zaman gidan amma ba su iyawa.
Me yasa shi ne kawai yake a matsanancin hali na rashin zaman lafiyar gidansa ne? 
 
Yana jin kamar ya mutu ko haka nan ya tuna matsalar gidansa, idan yaga abokansa na waya da matansu sai ya ji damuwa ta ziyarci zuciyarsa, shi bai san irin ai  wasa da dariya ba da matar aurensa ba, kowacce jin kanta take tamkar uwargijiyarsa ba mai ba shi kulawa balle ta dinga fitar da lokacin jin damuwarsa, kowace daga cikinsu ta kanta da yaranta kawai sai jiran ta ga gazawarsa ta ci mai mutunci ko da kuwa a gaban yaransa ne kuwa ba su jin damuwa suke ci mai mutunci son ransu babu guda ɗaya tilo da zai ware ya ce tana yi mai abin da yake so kowacce gani take bata da lokacin ba shi kulawa balle nuna mai tausayawa.
 
Maryam ganin bata ita yake ta gama gaya mai magana ta fice tana sakin tsaki ta banko ƙofar da ƙarfin tsiya.
 
Kawai fashewa ya yi da kukan fili mai ratsa zuciya, kuka yake yana jin ina ma ace shi ne Salim? Ina ace shi ne ya mutu ya barsu ba Salim ba ne ya mutu? Cikin kukan yake cewa, "Salim ka huta da matsalar mace, ka tafi baka ajiye kowace mace ba balle ace ka taɓa zubar mata da hawaye ka tafi salin alin ba baƙin cikin aure a zuciyarka na tayaka murna Salim dama ni ne na mutu ba kai ba."
 
Ya jima a yanayin kana ya tashi ya haɗa ruwa ya yi wanka ga yunwa dake addabar shi domin ba komai a cikinsa tun safe daya fita sai ruwan Lipton ya dawo ya ci abinci ne aka ɓata mai rai ya fasa cin abincin sai kuma abincin yasa suka kama faɗa kamar gidan mayunwata.
 
Allah Ya sani yana bakin ƙoƙarinsa na fita haƙƙinsu ko da yaushe yana ba su abinci yana ba su duk abin da ya kamata amma da yake so suke su wulaƙanta shi ga idanun mutane sai su dinga nuna bai masu komai, hakan yasa mutane ke zaginsa suna cewa bai iya riƙe aure gidansa yunwa ke akwai.
Yasha zuwa gaban Mamarsa ya yi ta kukan baƙin ciki domin abin na damunsa sosai kamar shi a dinga cewa gidansa ba abinci babu kaza babu kaza. Ko da yaushe mahaifiyarsa na jajanta mai ta yi mai nasiha ta kuma yi mai kyakkyawar addu'a daga ƙarshe ta rufe da mai albishir na samun wadda zata kula da shi duk daren daɗewa indai ya ƙara haƙuri domin Allah ba zai barshi a haka ba.
 
Kalaman iyayensa da danginsa kawai ke sawa yana samun natsuwa amma ba don haka ba da Allah kaɗai yasan yadda baƙin ciki zai maida shi sanadin matansa.
 
 
Tun daga ranar bai sake ganin Jiddah ba har ya amince da ta koma wannan karon ma bai amayar da abin da ke cinsa a rai ba game da ita ba, duk da cewar babu abin da ya sauya na daga halayen matansa sai dai a yanzu su biyu ne kawai suka rage ya saki amaryar tunda haka take buƙata ya gaji da zuwa ban haƙuri iyayenta da ita kanta na ci mai mutunci suna tozarta shi, don haka ya yanke shawarar sakinta duk da yasan hakan zai ƙara ma mutane ƙaimi gun ba shi baƙar sheda amma ya zai yi ? Ai Allah Yasan abin da ke faruwa kuma ba laifinsa ba ne ba.
 
Jiddah satin ta biyu ta koma gida, zuwa lokacin ta saba da Abubakar a waya ko da yaushe yana kiranta su sha fira duk da ba firar soyayya suke ba, domin ta gaya mai gaskiya ita ta gama soyayya don haka kar da ya ɗauka akwai so a tsakaninsu, shi kuma ya amince da hakan don haka alaƙar ta jima a tsakaninsu har aka koma makaranta sai suka yi wata irin muguwar shaƙuwa ta gasken-gaske wadda babu wanda zai yarda ba soyayya bace a tsakaninsu ba.
 
Domin dai Abubakar ya riga ya fahimci Jiddah mace ce mai son kulawa da nuna mata soyayya a zahiri tare da sakata a cikin nishaɗi ko da yaushe don haka sai ya yi amfani da damar wajen shiga jikin Jiddah ba tare da ita kanta ta ankara da hakan ba, sai dai ta wayi gari ta ganta cikin ƙaunarsa kawai ba tare da tasan daga ina ta faro soyayyar ba.
 
Da farko ta damu, amma daga baya data tuna da yadda yake sonta yake nuna mata kulawa ga gaban kowa nuna wa yake tafi kowa gunsa sai ta ji sauƙi ta ji ba komai bane don ta amince da soyayya da shi ba, don haka sai kawai ta saki jiki suka dinga wata irin soyayya mai ban mamaki wadda baki ɗaya makarantar kowa yasan Jiddah da Abubakar masoya ne.
 
Daga ita har shi babu mai kula wani da sunan soyayya sun yarda da juna sun amince da juna ko da yaushe tsara rayuwar aurensu suke idan suka gama karatunsu domin ya fita da aji biyu.
Duk wanda ya zo ga Jiddah da maganar soyayya kai tsaye zata ba shi haƙuri ta ƙare da ba shi labarin Abubakar da yadda suke son junansu, hakan yasa Jiddah bata da masoyi idan ba Abubakar ba, shi kaɗai ne burinta shi ne damuwarta shi ne fatanta, duk lokacin da ake maganar rashin cika alƙawarin maza kan aure Jiddah kan cire Abubakar a jerin mazan takan ce, "Shi ɗin na daban ne, haka yasan darajar soyayya da sanin martabar ta don haka bata ji ko da wasa Abubakar zai zama ɗaya daga jerin maza masu karya alƙawarin masoyansu.
 
Wasa-wasa Jiddah tai nisa a soyayyar Abubakar wanda hatta gidansu kowa yasan da zaman Abubakar a rayuwar Jiddah, zuwa yanzu Jiddah ta zama babbar ƴar kasuwa babu abin da bata saidawa, kasancewarta mai kyauta yasa ko da yaushe ita ce ke hidima da Abubakar bata damu da yadda suke ba, na yadda ko da yaushe kiran waya ne kawai ke haɗa ta da Abubakar ba wani kyauta ba komai, amma ita duk lokacin da ta saro kaya takan zaɓi wanda su kai mata kyau ta kai ma shi, hatta makaranta ita ce ke saimai duk abin da yake so ko ya nuna ko bai nuna ba, kuɗi ne kawai tsabar su bata iya ba shi, amma abin kuɗi ko ya kai na nawa tana iya ba shi kyauta.
 
Da dama ƙawayenta na yi mata faɗa kan hakan amma takan ce ita duk abin da tai ma Abubakar ba wani abu bane idan aka haɗa da yadda yake nuna mata soyayya da kulawa ba, don haka ita ba soyayyar kuɗi ce a tsakaninsu ba soyayyar aure ce a tsakaninsu don haka ya adana kuɗinsa idan su kai aure ya bata.
 
Babu irin shawara da zugar da ƙawayenta basu bata ba amma a banza jin su kawai take, duk lokacin data fahimci yana cikin matsalar wani abu takan yi mai abin kanta tsaye.
 
Yana yawan gode mata ya ce Allah Ya ba shi ikon cika burinsa kanta na yi mata alheri ninkin wanda take mai ko da yaushe amma ita bata son yana maganar ma sam.
 
Suna a haka ne ya nuna mata filinsa daya siya tai ta murna sosai domin tasan ita ce za a saka a gidan, hakan yasa ta hana shi kashe kuɗi wajen wasu abubuwan duk ta sake ɗauke mai nauyinsu ta cigaba da ba shi shawarar yadda za a gina gidan domin yana amsar kuɗin gwamnati na S POWER da ake biya duk wata-wata.
 
Nan da nan ya fara tara kuɗinsa ya fara haramai ginin gidansa wanda ko bulo aka siya sai ya nuna mata shi ta hoto abin na yi mata daɗi yadda Abubakar ke nuna mata komai na shi ita ce kan gaba, domin hatta tsarin gidan ita ce ta nuna mai yadda take son gidan nasu ya kasance kuma hakan ake yi komai yadda tace haka yake yin shi hatta shibkokin gidan duk ita ce ta zaɓi wanda take so a shuka mata kuma ya shuka mata su. 
 
Baki ɗaya ta sakankance Abubakar shi ne mijinta idan ta kammala karatunta domin shi a shekarar ƙarshe yake yanzu.
 
Wajen aikin su na polio aka ce an sake masu sabon S.T.P wanda bai da wasa don haka yanzu bata ƙalular zuwa gun aiki saboda kar ya je bata je ba ta samu matsala saboda tasan komai ta zama ta zama ne silar aikin polio don haka bata wasa da shi sam.
 
Ranar aikin tana zuwa bata jima da fara aikin ba sai ga S.T.P ɗin ya je gun su, kallo guda tai mai taga kamar tasan shi amma ta kasa tuna ina inda ta san shi don haka ta share kawai bayan sun gaisa ta cigaba da aikinta.
 
Sai dai kiran da yasa akai mata ne yasa ta fara tunanin shima ba mamaki ya san ta,  bayan sun gaisa ya kalle ta ya ce "Wai ba Jiddah bace ta gidan Hajjo ba?" 
 
Kanta ta ɗaga alamar ita ce, ya ce yana dariya, "Yanzu nan kin manta Ni? Ai ko muna yawan haɗuwa gidan ƙawarki Bilkisu domin ni ƙanin mijinta ne."
 
Tabbas an yi hakan yanzu ta tuna da hakan. Gaisawa suka sake yi tana dariya  ta ji kunyar yadda akai ta manta shi.
 
Bayan kwana biyu su kai waya da Bilkisu take gaya mata an turo ƙanin mijinta aiki garinsu shi ne Bilkisun ke ce mata don Allah ta taimaka tai mai magana ya sa ta aikin polio ita ma tun da yana da hanyar hakan ita kam kunya take ji.
 
Tace to ta tura mata lambar shi za tai mai magana insha Allah tun da ba lallai bane ba a sake maido shi garinsu aiki ba.
 
Sai kuwa ga lambar Bilkisu ta turo mata, kamar ta kira shi a lokacin sai kuma ta katse kiran ta bari sai anjima.
 
Da yake tana da application ɗin nan mai suna Trucoller sai taga sunan Mustapha madadin taga sunan Mubarak don haka sai abin ya ɗaure mata kai, sai kawai ta fasa kiran kawai ta cigaba da lamurranta kawai ta manta da lambar ma baki ɗaya a wayarta.
 
                      Bayan wani lokaci sai Jiddah ta sake komawa Kano domin dubo Hajjo da bata lafiya, bayan ta je gidan Bilkisu ne ta tuna da lambar da ta tura mata ta Mustapha kamar ta gaya mata lambar waye ta bata sai kuma ta share domin dai idan da arziƙi bai kamata ba ace yadda yake da Uncle Salim ba ta watsar da shi ba, kamata yai ace tana daraja shi tana kiransa suna gaisawa ko dan darajar abokinsa kuma ɗan'uwansa Uncle Salim ɗin ta.
 
Hakan yasa ta bar maganar kawai, musamman ita kuma Bilkisu da yake ta samu aikin sai batai mata maganar ba ita ma.
Bayan ta dawo gidan Hajjo ne ta gama komai ta kira Abubakar suka sha firar soyayarsu sai ta latsa lambar Mustapha da zummar kiransa ta gaida shi kawai.
 
Sai dai ta ji wayar a rufe don haka ta aje wayarta ta gyara kwanciyarta tana gode wa Allah yadda ya juya mata lamurranta daga zafafa zuwa sauƙaƙa daga ita har mahaifiyarta suna cikin rufin asiri ba su rasa komai ba, Mamarta na sana'ar saida robobi ita kuma tana tata sana'ar ga yaranta ta kaisu makaranta mai kyau hakan yasa take cikin kwanciyar hankali.
 
 
Har ta tafi basu haɗu da Mustapha ba, duk da cewar ta so su haɗu su gaisa domin hakan zai ɗebe mata kewar Uncle Salim sosai, amma basu haɗu ba kuma ta kasa sake kiran lambar wayarsa tun kiran farko da tai mai.
 
 
A ɓangaren Mustapha kuwa tun ranar da ta zo ya ganta sai dai a ranar aka tura shi Abuja gun wani aiki ba don ya so ba haka ya tafi yana jin tamkar zai rasa ta idan bai gaya mata abin da ke ranshi ba game da ita ba.
 
Ko da yake yanzu ya samu sauƙin lamurran sa tunda ya cire damuwar gidansa ya aje gefe guda sai dai idan su kai mai ya ji ciwon abin a ransa nan take da ya bar gidan ya manta, hakan yasa ya zama shahararre gun yawo a yanzu idan yabar gidansa da safe bai dawowa sai yamma idan zai wanka daga nan sai wajen sha biyu na dare yake dawowa ya haƙura da zaman gidan ya haƙura da cewa dole sai ya zauna da su yadda yake so ya bar su ne su zauna yadda su ya yi masu.
 
Duk wadda ta ga damar kula shi ta iske shi ɗakinsa shi dai ba zai kore ta ba, haka zai saurare ta amma ya daina biyewa ana jin muryarsa maƙwabta yana faɗa ya ƙyale su duk abin da su kai daidai da su ne.
 
Duk da haka ko da yaushe cikin masifa suke da junansu ba su daina tashin hankali ba haka basu daina zaginsa suna ganin yana tauye masu haƙƙi ba, kowacce gani take shi ne damuwarta shi ne bai kulawa da ita bai damu da farin cikinta ba, wannan yasa ya watsar da su baki ɗaya yake rayuwa tamkar marar mata yake rayuwa tamkar saurayi.
 
Iyarsa da su ya ajiye duk abin da yasan haƙƙinsa ne yana bakin ƙoƙarinsa kan hakan, amma su ya daina neman wani haƙƙi nashi kan su na wai su gyara gidansu da jikinsu ko yaransu duk ya daina haka ya daina ji a ransa cewar shi ya isa yasa ai mai abu a gidansa komai shi ke yin abinsa tun daga gyaran ɗakinsa linke kayansa da duk abin da ya danganci aikinsa shike abin sa.
 
Hutun makarantarsu ya ƙare kamar yadda su kai alƙawari da Abubakar zai fara komawa da kwana guda sannan ita ma ta koma , sai dai har akai kwana huɗu da komawa ba Abubakar ba labarinsa ko da yaushe a waya sai ya bata uzurin cewa hidimomi sun yi mai yawa ne , yanzu haka wayarsa ma ta lalace aron wadda yake kiranta da ita yake yana kiranta kuma bai da kuɗi domin an gama ginin gidan baki ɗaya kuɗin sun tafi can.
 
Hakan yasa ya bata tausai ta cire layukan wayarta ta aika mai da wayarta ita kuma ta siyi wata wayar.
 
Cikin lokacin sai waya tsakaninta da Abubakar ta ragu, sosai abin ke damunta sai tai ta kiransa a waya amma bai ɗauka, haka bai damu daya kira ta ba daga baya.
 
Kowa yasan Jiddah na cikin damuwa saboda ta sauya sosai, sai da Abubakar ya kira ta ya gaya mata cewar tai haƙuri ya rasa wayarsa ne babba sai ƙarama  don haka ko a chat bata ganinsa.
 
Ta yarda sosai da Abubakar don haka ta samu natsuwa da kwanciyar hankali kan lamarin har ta dawo daidai kamar baya.
 
 
Kasancewar ya ce mata bai da waya babba yasa bata damu da chat ba kawai sai idan ta kira shi ko ya kira ta take waya da shi kawai.
 
 
Wata ranar Litinin ta je makaranta duk ta damu da rashin dawowar Abubakar ana cikin sati na uku da komawa makaranta sai kira ya shigo wayarta kamar kada ta ɗauka don sabuwar lamba ce sai kuma ta ɗauka.
 
"Salamu alaikum, ina magana da Jiddah ne don Allah?"
Daga can ɓangaren aka tambayeta, kamar mai maganar yana gabanta haka ta girgiza kanta. Zuwa can ta amsa da cewa "E Ni ce Jiddah ke magana."
 
 
"To Jiddah don Allah ki yi haƙuri ba ki san Ni ba amma Ni nasan ki, ina so ne na gaya maki abin da ke faruwa kan alaƙarki da Abubakar, ko kin san cewa Asabar ɗin nan data wuce aka ɗaura mai aure? Nasan za ki yi mamaki amma ki je facebook ki duba za ki ga hotunan auren ki duba page ɗina domin duk mun saka har dana amaryar ma."
 
 
Kawai wayar faɗuwa tai daga hannunta ba tare da tasan lokacin da hakan ya faru ba, rabon da taji alamar hawan jininta ya tashi ko zai tashi har ta manta amma nan take ta dinga jin kanta na sarawa numfashinta na fita da ƙyar.
 
Kamar mahaukaciya haka ta warto wayar ta kunna data ta shiga facebook ta duba sunan Abubakar ɗin amma bata ganshi ba, hakan yasa ta fahimci ya yi blocking nata don haka sai ta saka sunan abokinsa da ya kira ta.
 
Kamar a mafarki haka ta ga hotunan Abubakar da amaryarsa wani kuma da abokansa, tun daga na wajen ƙwallon amarya da ango har na wajen ɗaurin aure har da na walima duk an ɗora.
 
 
Kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata bata san lokacin data yanke jiki ta faɗi gun ba.
 
 
To masu karatu mu haɗu a kashi na gaba don jin yadda zata kaya.
 
Me yasa Abubakar ya yi mata hakan?
 
 
Taku a kullum Haupha ✍️ kuma