Ɗaruruwan Matasa  Sun Sauya Sheka Daga APC  Zuwa NNPP

Ɗaruruwan Matasa  Sun Sauya Sheka Daga APC  Zuwa NNPP

A ranar Lahadin da ta gaba ne dai dandazo matasa a unguwar Fagge D2 da ke karamar hukumar Fagge ta jihar Kano, suka sauya sheka daga jamiyya mai mulki ta APC zuwa jamiyyar NNPP. Taron wanda aka yi shi karkashin jagorancin dan takarar majalisar tarayya na Fagge Barrister MB Shehu Fagge da dan majalisar jiha mai ci kuma dan takarar majalisar jihar Hon. Tukur Muhammad da MD na kamfen dinsu, Hon. Ibrahim Provost da shugabannin jamiyyar NNPP na Fagge D2 da shugabannin Kwankwasiyya na Fagge D2 da masu ruwa da tsakin jamiyyar,

Taron  ya samu halartar dimbin matasa maza da mata da dattijan unguwar, 

Matasan wadanda yan gwagwarmaya da jajurcewa ne ta fuskar cigaba a mazabar Fagge D2 da unguwar Fagge, a da suna bin tsarin jamiyyar APC ne a karkashin dan majalisar tarayya mai ci Hon. Aminu Suleiman Goro, sun dauki wannan matakin ne a karan kansu ba tare da an yi zawarcinsu ko neman su bar jamiyyar APC ba,

Matasan dai sun ce ba su gani a kasa ba, wanda  su ka ce burinsu shi ne su ga ci gaban wannan mazaba da unguwar Fagge da Kano bakidaya.

Daruruwan matasan sun bayyana zaman da suka yi a jamiyyar ta APC karkashin shi dan majalisar a matsayin zaman daurin-zato da ake yi wa alummar Fagge gabadaya. 

A cewarsu, da yawan  matasan an cika su ne  igiyar zaton cewa za su rabauta da aikin yi amma suka ji shiru.