Ɗangote ya ɗaukarwa 'yan Nijeriya alƙawali kan man Fetur
Akwai Yiyuwar farashin man fetur ya sauka Dangote ya sha alwashin wadata yan Najeriya da wadataccen mai daga kasashen waje.
Matatar man Dangote na kara gina wasu tankokin yaki guda takwas a yunkurinta na samun isasshen wurin ajiyar danyen mai daga kasashen waje.
Wani rahoto da Africa Report ya fitar ya nuna cewa matatar man tana kara habaka karfin ajiyarta da ganga miliyan 6.29, kwatankwacin lita biliyan 1.
Rahoton ya bayyana cewa matatar ta dala biliyan 20 na shirin tara danyen man da aka shigo da su daga kasashen waje saboda kayan da ake samu a cikin gida sun zama marasa aminci.
An ruwaito jami’an matatar na cewa karancin danyen da ake samu daga Kamfanin Man Fetur na Najeriya Limited “yana haifar da dogaro da shigo da kayayyaki daga waje.
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
managarciya