Hare-Haren 'yan bindiga suna addabar mutanen Zamfara a Kwanannan
Hare-haren ‘yanbindiga sun sake kunno kai a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, bayan kwashe wani lokaci mai tsawo ana samun saukin matsalar tsaron.
A baya-bayan nan ‘yanbindigar sun kai hari wasu garuruwa na yankin karamar hukumar Bukkuyum.
Ko a 'yan kwanakin nan wasu 'yanbindiga sun kai hari garin Gana, inda suka kona gidaje da kayan abinci, suka yi awon gaba da mata arba'in da biyar da namiji daya, baya ga kashe wani mutum, kamar yadda BBC ta samu bayani.
Danmajalisar Wakilai na Najeriya mai wakiltar kananan hukumomin Gumi da Bukkuyum a jihar ta Zamfara, Dakta Sulaiman Abubakar Gumi, ya shaida wa BBC, cewa da fari ana ta murna an samu saukin lamarin, amma kuma yanzu matsalar ta sake kunno kai.
“Matsalar ta dawo kusan ma fiye da baya, saboda an dade ba a far wa gari a kona muhallansu da kayan masarufinsu ba kamar wannan lokacin. A Ranar Talata sun far wa wasu garuruwa sannan sun sace mata 40 da namiji daya a kasar Gana da ke karamar hukumar Bukkuyum, sun kuma kashe mutum guda,” in ji Gumi.
Dakta Sulaiman ya kara da cewa a makon da ya wuce, 'yan ta’addar sun sace mutane 20 bayan artabun da suka yi da ‘yansakai da jami’an tsaro a kokarin ceto mutanen, har mutum gudu ya mutu inda su ma ’yanbindigar aka kashe nasu mutanen.
”Sun yi abin da suka yi, don sun kona kusan garin, gidaje kadan ne suka rage. Mutanen na cikin halin kaka-ni-kayi saboda an kone musu kayan abinci, hatta uban kasa na garin an sace iyalinshi.”
Ya danganta sake kunno kan hare-haren ‘yanbindigar a jihar da aikin da ‘yansakai ke yi na kama masu tsegunta wa ‘yanbindiga bayanai, inda ya ce, daman sukan yi haka idan an kama mutanen su.
Dan majalisar ya kara da cewa a bangarensa na wakilin jama’a sun fara kokarin kai musu dauki na kayan abinci kafin gwamnati ta kai nata.
Ya yi kira ga gwamnatin jiha ta yi kokarin kai musu dauki, musamman na abinci ganin halin da suke ciki, da alkawarin gabatar da koke gaban majalisa da zarar an koma bakin aiki domin kara tallafawa da maganar matsalar tsaron a jihar ta Zamfara.
managarciya