Matsalar Tsaro: Gwamnan Yobe Ya Gana Da Tinubu

Matsalar Tsaro: Gwamnan Yobe Ya Gana Da Tinubu

 

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa don tattauna matsalar tsaro da ta addabi jiharsa. 

Daraktan watsa labarai na gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed ya fitar da sanarwar hakan, inda ya ce Buni ya kuma hadu da ministan harkokin 'yan sanda, Sanata Ibrahim Gaidam. 
Gwamnan da ministan sun tabbatar da cewa an samu tsaro a 'yan kwanakin nan, amma sun duba yiwuwar kawo sabbin tsare-tsare na inganta tsaron a fadin jihar.
Leadership ta ruwaito cewa Buni da Gaidam sun garzaya fadar shugaban kasar, inda suka tattauna da Shugaba Tinubu, kan hanyoyin kawo karshen matsalar tsaro a Yobe. Gwamnan ya ce: "Duk da an samu tsaro a jihar, sai dai akwai garuruwan da ke iyakokin jihar da ke fuskantar hare-hare, mun dauki matakan dakile 'yan ta'adda daga shigowa cikin jihar." 
"Ba shakka an samu tsaro a Yobe, musamman cikin birane, sai dai har yanzu wasu kauyuka na fuskantar barazanar 'yan ta'adda." 
A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa gwamnan cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiyuwa don inganta tsaro a Najeriya, a cewar rahoton Independent.