Ɗan Takarar Sanata A Jam'iyar APC A Jigawa Ya Rasu

Ɗan Takarar Sanata A Jam'iyar APC A Jigawa Ya Rasu
 
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da al'ummar jihar Jigawa bisa rasuwar Alhaji Tijjani Ibrahim Gaya, dan takarar kujerar Sanata na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen 2023.
Alhaji Mohammed Badaru ya bayyana Ibrahim Gaya a matsayin mutum mai mutunci, babban jagora, kuma abin koyi ga matasa masu tasowa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya domin yiwa talaka hidima.
“Rasuwar Tijjani Ibrahim Gaya ta zo da matukar kaduwa a gare ni da kuma al’ummar Jihar Jigawa. Dole ne kowane rai ya ɗanɗana mutuwa. 
A kullum addu’ar mu ita ce mu yi kyakkyawan karshe kuma babu shakka dan uwanmu ya gama da shi lafiya bayan ya yi fama da doguwar jinya.” Gwamnan yace.
Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya jikan marigayin da Jannatul Firdausi, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin.
Kwamishinan Ayyuka na Musamman Auwal D. Sankara ya fitar da bayanin ga manema labarai a daren Assabar.