‘Yan bindiga na cin karensu ba babbaka a jihr Sakkwato
Aiyukkan ta’addanci na ‘yan bindiga ya kara ta’azara musamman a Gabascin jihar Sakkwato in da kananan hukumomin Isa da Sabon Birni da Tangaza da Binji ke shan bakar wahala kan hare-haren ‘yan bindigar ba kuma wani takamanmen mataki daga bangaren jami’an tsaro da gwamnatin jiha.
Sama da wata daya da ‘yan bindigar suka yi ta kai hare-hare bayan lafawar da aka samu tun bayan kammala babban zaben 2023 yanzu matsalar ta dawo sosai a kananan hukumomin in da mutane suke cikin mawayacin hali kai ka ce ba gwamnati.
Ana Kara samun yan gudun hijira dake shiga kasar Nijar neman mafaka kuma yanzu ga matsalar rufe boda da aka samu wadda ya kara ta'azara wahala da dimaucewa a tsakanin jama'a kan rashin mafita da ta dabaibaye su waton rana zafi inuwa Kuna.
Malam Bashar Altine Guyawa Isa daya daga cikin ‘yan asalin karamar hukumar Isa ne ya yi Magana kan halin da suke ciki ya ce yakamata hukumomi su sani wannan halin yau shekara 11 suna cikinsa, dole a yanzu talakawa su yi magana domin hukuma da mutanen da suka zaba sun kasa, matsalar tsaro bata shafi siyasa ba abu ne da ya shafi mutane gaba daya duk mai ganin magana kan tsaro siyasa ce yana zolayar kansa ne kawai.
"sati biyu da suka wuce zuwa yanzu matsalar tsaro ta kara ta'azara a yankinmu an yi kwana uku a jere karamar hukumar Isa ba a barci dukkan kauyukkan da ke zagaye da ita sun zagaye su duk mutanen da ke cikin wuraren karkashin 'yan bindiga suke rayuwa, a kalla sama da mutum 30 na hannunsu.
"Bayan cikin garin Isa ba in da ake karatun boko dukkan karamar hukumar 'yan bindigar sun hana, al'ummar garin cikin kashi uku babu biyu cikinsu wasu sun bar garin an kashe wasu, an kideme an rude, ana kashe mu a fili amma matakan hana a kashe mu an boye su don kawai wasa da hankalinmu ba a yin abin tausaya mana, ba a zuwa cikinmu" a cewar Guyawa Isa.
Ya ce noma gaba daya babu shi a karamar hukumar kamar yadda ba a karatun Furamare a can. "domin mafiyawan 'yan bindigar dake addabar Arewa anan suke da sansani ganin ba a wani fada da su tun daga kan Turji da Baleri da Dogo Gide har kan Lakurawa da ke fitowa gefen Tangaza. A tsakanin Isa da Sabon Birni mutanen da ake garkuwa da su sun fi 100, an kassara noma da kiyo"in ji shi.
Dan majalisar dokoki dake wakiltar karamar hukumar Isa Habibu Halilu Modachi ya ce matsalar tsaro ta dade ana fama da ita a yankin Isa da Sabon Birni gwamnatin data gabata ta kasa magance matsalar ga shi wata ta shigo abubuwan ba a bari ba, a matsayinmu na 'yan majalisa mun kai kukanmu ga gwamnati amma ba abin da aka yi yanzu kura ta kai bango a karamar hukumarmu kowace safiya 'yan bindiga na nan ba su saki kafa ba a daji ne da cikin gari suna daukar mutane domin neman kudin fansa.
"Wannan gwamnati ta fito fili ta fadi Gwamna da kansa ya fadi ko kudin jiha za su kare a sha'anin tsaro zai kashe su kowa ya ji ya fadi, tau wane mataki aka dauka a ga tsare-tsare kowa ya ba da tasa gudunmuwa a cire siyasa hakan zai magance matsalar tsaro a Sakkwato.
"Akwai siyasa a yanzu in ba fitar da ita ba harkar tsaro ba zai kare ba, mu ne wakilan jama'a in har akwai wasu tsare-tsare da ake yi dole ne mu sani tun sanda aka rantsar da gwamnatin nan ba wani shiri kan tsaro da muka ga ta yi a Sakkwato baki daya.
"Matsalar tsaron Isa kowa ya san da ita, duk shugaban riko da za a samu a shugabancin karamar hukuma yakamata ya mayar da hankali kan tsaro ganin yanda ilmi ya tabarbare a fusakanci matsalar kai tsaye a ceto yankin gabascin Sakkwato, don Allah a yi abin da yakamata domin ceto al'ummarmu."
Malami a jiha Malam Murtala Bello Asada a wurin wazinsa ya nemi da gwamnatin Sakkwato ta ji tsoron Allah kan tsaron jiha ya ce "Sakkwato ko hagu ba a samu balle dama halin da gabascin Sakkwato yake ya kamata Gwamna ya ji tsoron Allah ya ce in kudi jiha za su Kare zai sa su a tsaro, ko naira ba a sa ba, a cikin sati daya an yi garkuwa da mutane sama da 30 a cikin garin Isa."
Ya ce ana yi wa Gabascin Sakkwato bala'i Amma an kyale su, yakamata gwamna ya tafi wurin shugaban kasa tare da sanatocin jiha da Sarkin Musulmi domin a dauki matakin abin ya yi yawa.
managarciya