Kungiyar Malaman Kwalejojin fasaha ASUP na shirin tsunduma yajin aiki

Kungiyar Malaman Kwalejojin fasaha ASUP na shirin tsunduma yajin aiki

Kungiyar malaman kwalejojin fasaha ta ASUP ta bai wa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 15 don biya mata bukatun ta, inda tayi gargadin fara yajin aiki idan ba a samu wani ci gaba ba.

Mista Shammah Kpanja, shugaban kungiyar ASUU na kasa ne ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da ya gudana bayan taron koli na kungiyar a Abuja ranar Alhamis.

Kpanja yayi bayanin cewa kwanakin zasu fara daga 7 ga watan Oktoba kuma sun zama  dole duba da gazawar gwamnatin wajen aiwatar da batutuwa masu yawa da suke shafar fannin ilimin kwalejin fasaha.

Sannan ya bukaci shugabannin shiyya na kungiyar ta ASUP da su shirya mambobin su don yiwuwar daukar matakin  yin zanga zangar lumana don jawo hankalin gwamnati kan bukatun su.

Kungiyar dai na nuna damuwa kan yadda gwamnati ta dau wasu matakai da suka ci karo da dokar kafa kwalejijon fasaha na tarayya.

Sannan sun koka kan yadda wasu jihohi suka ki aiwatar da tsarin karin albashi ga mambobin su.