Kasafin 2025: Tinubu ya ware Naira Biliyan 6,364,181,224, na gyaran gidan gwamnati
Gwamnatin Najeriya ta ware naira biliyan 6,364,181,224 domin gyaran gidajen shugaban kasa, Bola Tinubu, mataimakinsa Kashim Shettima, da wasu mataimakansu a kasafin kudin 2025.
Binciken da jaridar Sunday PUNCH ta yi a kan shirin rabon da ke kunshe a cikin kudirin kasafin kudi na shekarar 2025 da aka gabatar wa majalisar dokokin kasar, ya nuna cewa gyaran da ake yi a fadar shugaban kasa a duk shekara zai ci Naira biliyan 5.49
A cewar kasafin kudin, Naira miliyan 765 za a yi amfani da shi wajen gyara rukunin mataimakin shugaban kasa da kuma masaukin baki.
Daga Abbakar Aleeyu Anache
managarciya