Ɗan Ƙwallon Nijeriya  Abdullahi Shehu  Ya Ziyarci  Tambuwal A Sakkwato

Ɗan Ƙwallon Nijeriya  Abdullahi Shehu  Ya Ziyarci  Tambuwal A Sakkwato

Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto.  

A kokarin da yake yi na inganta da habaka harkokin wasanni a jihar Sokoto da kasa baki daya, dan wasan ƙwallon ƙafa na Nijeriya, Abdullahi Shehu ya ziyarci Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal domin cigaba da tattaunawa akan habaka shaanin wasanni a jihar Sokoto.

Abdullahi shehu ya bayyana cewa a lokacin ziyarar an tattana muhimman abubuwa musamman hanyoyin da za a kara habaka harkokin wasanni, tattalin Arzikin jihar,samar da ayukkan yi ga matasa,  da suran kasuwanci a mahaifar ta shi.

Ya bayyana cewa wannan ziyarar zata haifar da da mai ido a wajen cigaban jihar domin zasu hada hannu dan ciyar da jihar gaba, kamar yadda ya bayyana ashafin na Facebook.