Kungiyar Kwallon Kafa Ta Kano Pillars Ta Fara Gasar Firimiya Da Rashin Nasara

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Kano Pillars Ta Fara Gasar Firimiya Da Rashin Nasara

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Kano Pillars Ta Fara Gasar Firimiya Da Rashin Nasara

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Akwa United ta mai riƙe da kambun gasar Firimiya ta NPLF ta Nigeriya ta lallasa Kano Pillars da  3-0 da aka fara ranar Lahadin da ta gabata,

Pillars, wacce ake yi wa laƙabi da Sai masu gida, ta sha kashi ne a gidan Akwa United a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.
 
Ezekiel Bassey ne dai ya fara zura ƙwallo a ranar Pillars a minti na 45, a na daf da tafiya hutun rabin lokaci.
 
Jim kaɗan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, a daidai mintuna na 53 sai Stephen Chukwude shi ma ya jefa tashi ƙwallon.
 
Ya yin da a mintunan  ƙarshe na tashi daga wasan ne kuma Ubong Friday ya rufe taro da addu'a, inda shi ma ya zura tashi ƙwallon da ta baiwa Akwa United nasar samun maki 3 da kuma ƙwallaye 3 a gasar ta bana.