Babu Tabbacin Zaben 2023 Zai Gudana----Hukumar Zabe

Babu Tabbacin Zaben 2023 Zai Gudana----Hukumar Zabe

 

Za a Iya Samun Matsalar Soke Zaben 2023 Saboda Rashin Tsaro, INEC 

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi gargadin cewa, zaben bana da ke tafe nan da wata guda zai iya samun tasgaro saboda yawaitar rashin tsaro a Najeriya. 
A cewar hukumar, akwai yiwuwar a samu barazanar soke zaben matukar matsalolin tsaron kasar suka ci gaba da faruwa. 
Wannan batu dai na fitowa ne daga shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmud Yakubu yayin da ya zamu wakilcin shugaban cibiyar zabe ta BEI, Farfesa Abdullahi Abdu Zuru a ranar Litinin a Abuja. 
Zuru ya yi gargadin ne a wani taron horarwa kan tsaron zabe da aka gudanar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. 
A cewarsa, hukumar zabe na aikin da ya dace don tabbatar da an yi zabe lafiya kuma cin lumana, amma idan aka yi rashin sa'a matsalolon tsaro suka ci gaba da ta'azzara, hukumar za ta san na yi. 
A kalamansa: "Bugu da kari, idan ba a sanya ido kan lamarin tsaro kuma aka magance shi ba, zai kai makuran da za a soke zabe ko kuma dage shi a wasu mazabun masu yawa don gujewa matsala ga sakamakon zabe da kuma rikicin kundin tsarin mulki da ka iya faruwa baktatan. 
A bagare guda, Zuru ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa hukumomin tsaro kama da kan mai ba shugaban kasa shawari har shugabannin hafsoshin tsaro sun ba 'yan Najeriya tabbacin za a yi zaben 2023, Punch ta ruwaito. 
Hakazalika, ya ce hukumar ta zaben zaben na yin duk mai yiwa don tabbatar da an yi zaben kana an fitar da sakamako daidai da yadda sabon kundin zabe na 2021 ya tanada.