Albashi Na Neman Ya Gagara A Sakkwato
Mai yuwuwa jihohi 33 a Najeriya ba za su iya biyan albashi ba cikin kuwa hadda jihar Sakkwato, saboda shirin gwamnatin tarayya na fara yanke kudin da take biya bashi, a yanzu ta zaftare bashin dala miliyan 418 kwatankwacin naira miliyan 172 na kungiyar masu bayar da bashi waton Paris Cub.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, matsayin jihohi (‘State of States 2019'), BudgIT, wadda kungiya ce da ke sa ido kan harkokin kudi na gwamnati ta ce gwamnatocin jihohi uku ne kawai - Lagos da Rivers da Akwa Ibom, za su iya biyan albashi da sauran harkokinsu na yau da kullum ba tare da samun kason gwamnatin tarayya ba.
Kungiyar gwamnonin Najeriya da sauran al'ummar kasar na matsa lamba domin dakatar da biyan wadannan kudade da ake gani ba na gaskiya ba ne ga kwararrun.
Sai dai kuma a wani abu da ke bayar da mamaki, kasa da wata daya bayan da Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni, ma'aikatar kudi da kasafi da kuma tsare-tsare ta fara zaftare kason kudaden da ake bai wa jihohi na kananan hukumomi domin biyan bashin aka dabbaka umarnin.
Babban sakatare na ma'aikatar ya gaya wa taron kwamitin rabon kudade na tarayya a ranar Juma'a cewa, ma'aikatar ta fara yanke kudaden domin biyan bashin.
Wannan bayani ya harzuka jihohin, suka ki yarda da rabon watan Oktoba da ake ciki, har sai gwamnati ta dakatar da wannan kudirin nata.
Wasu na kallon a wannan lamarin gwamnonin Nijeriya ba su da gaskiya kan lamarin domin sun san bashi ne aka ba su domin su gyara wasu matsalolin jihar su kuma koyaushe ne dai za a nemi a biya bashin.
Tun da har gwamnatin tarayya ta ce za ta cire kudinta ai kawai su yi hakuri su nemi wata hanya domin tafiyar da gwamnati ba tirjiya ba.
Gwamnatin tarayya ta ba su tallafin Paris Club da Bailout ta kuma biya bashin da jihohi ke bi a gwamnatin tarayya na aiyukka da gwamnatocin da suka gabata suka yi, a wadan nan aiyukkan ne yakamata su gina jihohinsu ta hanyar tattalin arziki kafin haka.