ECOWAS Ta Sanya  Sabbin Takunkumi A Jamhuriyar Nijar 

ECOWAS Ta Sanya  Sabbin Takunkumi A Jamhuriyar Nijar 

 

Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) ta sake sanya sabbin takunkumi kan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar. 

Ƙungiyar ta ECOWAS tun da farko ta ba sojojin da suka yi juyi mulki a ƙasar wa'adin kwana bakwai na su mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan muƙaminsa, ko ta ƙaƙaba musu takunkumi ciki har da amfani da ƙarfin soja. 
Amma sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi biris da barazanar ECOWAS sannan suka sha alwashin daƙile duk wani shiga tsakani daga ƙasar waje da za ayi a Nijar. 
Da yake tattaunawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa a ranar Talata 8 ga watan Agusta, kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa an ƙara sanya takunkumi akan masu hulɗa da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, rahoton Daily Trust ya tabbatar. 
Duk da dai bai yi cikakken bayani ba, ya bayyana cewa an yi hakan ne ta hannun babban bankin Najeriya (CBN).