Tsohon gwamna ya soki Tinubu kan sayen sabon jirgin sama
Tsohon gwamnan jihar Cross River, da ke kudu maso kudancin Najeriya, Donald Duke, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan sayen sabon jirgin sama, a lokacin da 'yan kasar ke fama da yunwa, da cewa alama ce ta gazawar gwamnati.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Mista Duke, wanda ya kasance gwamnan jihar ta Cros River a tsakanin shekarun 1999 da 2007, ya faɗi hakan ne a lokacin hira da tashar talabijin ta Channels a yau Juma'a.
Ya ce: ''Babu wata birgewa ka ce mutanenka na fama da matsalar rayuwa; gazawar shugabancinka ne. Idan ni ne shugaba a gida, zan so a ce iyalina suna da komai, ba zan so a ce suna cikin matsin rayuwa ba.''
''Idan rayuwa ta yi tsanani, to zan ji na kasa sauke nauyin da ya rataya a wuyana a kansu. Ina shawartarsa da ya ɗauki al'ummar Najeriya a matsayin iyalinsa. Abin da yake alheri ga iyalinsa alheri ne ga ƙasar,'' ya ce.
A makon da ya wuce ne babban mai taimaka wa shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa gwamnatin ta sayo sabon jirgin saman ƙirar Airbus A330, domin maye gurbin wanda ake da shi Boeing B737-700, mai shekara 19, wanda tun a zamanin mulkin Obasanjo ya sayo.
A kan maganar tsaro da ƙasar ke fama, Mista Duke, ya ce kamata ya yi shugaban ya tuhumi shugabannin hukumomin tsaro.
Ya ce ba ta yadda za ka zauna ka ce kai ne DPO ko kwamishinan 'yansanda ko shugaban sojoji kuma ana aikata laifi a yankinka. Ka tuhume su.”
managarciya