Gwamnatin Tarayya Ta Tallafawa Manoman Alkama 2500 A Neja

Hajiya Hassana Muhammed, ita ce wakiliyar babban bankin Najeriya mai kula da noman Alkama, ta janyo hankalin manoman akan  karkatar da tallafin da suka samu ba za a lamunce hakan ba, domin gwamnatin tarayya ta kirkiro shirin ne don yaki da talauci da bunkasa abinci a kasa, ta hanyar karfafa guiwar manoman. Jami'ar ta ce za su cigaba da sanya idanu musamman ganin wannan shirin na daga shiraruwar gwamnatin tarayya kan noman rani, wanda bukatar farfado da noman Alkama a kasar nan. Da yake karin haske ga manema labarai, shugaban kungiyar manoma Alkama a jihar Neja, Ambasada, Dakta Nura Hashim, ya ce an ware hekta dubu biyu da dari biyar dan yin noman. Ya cigaba da cewar 'za mu cigaba da sanya idanu ga manoman lokaci zuwa lokaci dan ganin halin da anfanin gonar zai kasance, da kuma samun nasarar noman a jiha.'

Gwamnatin Tarayya Ta Tallafawa Manoman Alkama 2500 A Neja

 

 

Daga Babangida Bisallah, Minna

 

 

A yunkurin gwamnatin tarayya na dawo da martabar noma a kasar nan, ta tallafawa manoman Alkama da kayan aikin noma su dubu biyu da dari biyar  a jihar. Shirin gwamnatin tarayya wanda babban bankin Najeriya(CBN) ke kula da shi. 

Kwayar Alkama tana daya daga cikin anfanin gona da yake da tasiri a kasar noman jihar, ya janyo hankalin babban bakin Najeriya, na baiwa manoma 2500  tallafin kayan noma.

Maoman da suka fito daga Ghaze na karamar hukumar Edati da Loguma da ke karamar hukumar Agaie na daya daga cikin kashin farko da suka fara cin anfanin tallafin.
Manoman sun samu tallafin takin zamani, injimin ban ruwa, irin shuka da sauran kayan aikin noma.

Hajiya Hassana Muhammed, ita ce wakiliyar babban bankin Najeriya mai kula da noman Alkama, ta janyo hankalin manoman akan  karkatar da tallafin da suka samu ba za a lamunce hakan ba, domin gwamnatin tarayya ta kirkiro shirin ne don yaki da talauci da bunkasa abinci a kasa, ta hanyar karfafa guiwar manoman.
Jami'ar ta ce za su cigaba da sanya idanu musamman ganin wannan shirin na daga shiraruwar gwamnatin tarayya kan noman rani, wanda bukatar farfado da noman Alkama a kasar nan.
Da yake karin haske ga manema labarai, shugaban kungiyar manoma Alkama a jihar Neja, Ambasada, Dakta Nura Hashim, ya ce an ware hekta dubu biyu da dari biyar dan yin noman. Ya cigaba da cewar 'za mu cigaba da sanya idanu ga manoman lokaci zuwa lokaci dan ganin halin da anfanin gonar zai kasance, da kuma samun nasarar noman a jiha.'
Ya ce "gwamnatin tarayya ta kashe kudi mai yawa wajen kawo wannan irin daga waje, saboda anfanar manoma, muna da yalwataccen kasar noman Alkama a jihar nan, wanda idan muka mayar da hankali akan noman alkama kawai za mu samar da kasuwa mai anfani da zai anfanar da tattalin arzikin kasar nan.

Saboda haka za mu tabbatar mun bi wadanda suka samu tallafin kai da fata dan ganin sun yi anfani da shi yadda aka tsara."
Malam Abdullahi Muhammed, daya daga cikin wadanda suka samu tallafin, ya bayyana farin cikinsa akan zabinsa da kungiyar ta yi dan ganin ya ci wannan gajiyar, dan haka zai yi anfani da wannan tallafin noman wajen inganta rayuwarsa, ta hanyar anfani da tallafin yadda ya dace.
Tallafin noman, wanda shiri ne na gwamnatin tarayya a baiwa manoma rancen kayan anfanin gona, wanda idan suka noma suka girbe za su biya kudin kayan da babban bankin ta ba su.