Tarabunal Ta Tabbatar da Nasarar Sanata Lamido Tare da Cin Tarar Gwanda Gobir

Tarabunal Ta Tabbatar da Nasarar Sanata Lamido Tare da Cin Tarar Gwanda Gobir

Kotun sauraren korafin zabe mai zamanta a Sakkwato a yau Jumu'a ta yi watsi da Karar da Dan takarar Sanata a yankin Sakkwato ta Gabas Alhaji Shu'aibu Gwanda Gobir da PDP suka  sa a gabanta in da suke kalubalantar nasarar da Sanata Ibrahim Lamido da APC  suka samu a babban zaben 2023 da ya gabata.
Alkali Emanuel A. Ubua ne ya karanta hukuncin a madadain sauran alkalan ya ce sun yi watsi da Karar ne domin rashin cancanta don sun kasa gamsar da kotu a jerin  hujjojin da suka gabatar.
PDP da Dan takararta suna kalubalantar cancantar Lamido ne in da suke zargin bai yi karatun Furamare da Sikandare ba, Kuma sunan da yake amfani da shi akwai Wanda ba nasa ba, a wurin zaben an sabawa dokokin zabe a rumfuna da dama a yankin Gabascin Sakkwato.
Rashin gamsar da kotu Mai Shari'a ya Kori Karar kan rashin cancanta ya Kuma nemi masu Kara da su biya tarar Miliyan Daya domin bata lokacin da aka yiwa Sanata.
Bayan kammala shari'a Sanata Ibrahim Lamido ya godewa magoya bayansa da al'ummar Sakkwato baki daya kan jajircewarsu na tabbatar da ya samu nasara a cikin Kowace tafiaya.
Sanata Lamido ya ce wannan nasarar da aka samu ta muce gaba daya yankin Gabascin Sakkwato ganin yanda kotu ta tabbatar da abin da suka zaba, hakan zai kara taimakon yankin a bangaren cigaban da ake samu.
"Ina kira ga abokin takara ta da ya ajiye adawa gefe ya zo a hada hannu don ceto yankinmu a halin rashin tsaro da matsin rayuwa da ake fuskanta.
"Zabe ya zo ya tafi Wanda Allah ya ba nasara sai a zo a hada Kai da shi don samun cigaba, al'umma ba su bukatar jayayya tsakanin 'yan siyasa, hada Kai suke so don ganin an tsamo su a halin da suke ciki a yau." Kalaman Lamido.
Ya kara tabbatarwa mutanen da yake wakilci za su cigaba da samun romon dimukuradiyya a gefensa da jam'iyar APC a kasa da jiha baki daya.
"Ina ba da gudunmuwa sosai kan tsaro da inganta muhalli da samar da fitillun haska wurare sola da tallafin karatu da saura su," in ji Lamido.