Na ziyarci sakataren gwamnatin tarayya ne don cigaban Sakkwato---Sanata Lamido

Na ziyarci sakataren gwamnatin tarayya ne don cigaban Sakkwato---Sanata Lamido
Sanata Ibrahim Lamiɗo ya ziyarci sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume a fadar shugaban kasa in da suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yankin da yake wakilta da jihar Sakkwato baki daya.
A ziyarar da yakai a jiya Talata Sanata Lamido ya shaidawa manema labarai makasudin ziyarar don tabbatar da cigaban jihar Sakkwato ne.
"Na kai ziyarar don ganin jihar Sakkwato ta samu cigaba a cikin shiraruwan da gwamnatin tarayya ke fitarwa da suka shafi gina kasa da al'umma.
"Kar ka manta har yanzu yankina na Sakkwato ta gabas na fuskantar matsalar tsaro da ya kawo tabarbarewar harkar ilmi da kasuwanci. Dole ne mu rika zama da manyan jami'an gwamnati don jawo hankalin su ga tsananin bukatar da mutanenmu ke da ita," a cewar Sanata Lamiɗo.
Ya kara da cewar ziyarar nada nasaba da wakilcin da yake yi don tabbatar da ya kawo cigaba ga jihar Sakkwato.