2023: APC Da PDP Za Su Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Da Gwamnoni A Watan Agustan 2022

Haka kuma sunayen 'yan takarar gwamna a dukkan jam'iyyu za a hannunta su ga hukumar zabe a watan na Augusta. Shugaban hukumar zabe na kasa Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da cewa zaben shugaban kasa za a gudanar da shi 18 ga Fabarairun 2023, hukumar za ta fitar da jadawalin harkokin zaben bayan kammala zaben Anambra wanda ya gudana a 6 ga watan Nuwamba.  Akwai yiyuwar a samu sauyin ranar zaben 'yan takara bayan shugaban kasa ya sanya sabuwar dokar zabe da aka yi wa gyaran fuska hannu, an kai wa shugaban kasa dokar wadda ake zaton zai sanyawa hannu kowane lokaci daga yanzu.

2023: APC Da PDP Za Su Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Da Gwamnoni A Watan Agustan 2022

2023: APC Da PDP Za Su Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Da Gwamnoni A Watan Agustan 2022

 

A tunkarar babban zaben 2023 akwai alamu mai karfi da ke nuna jam'iyar PDP da APC da sauran jam'iyyun siyasa da za su shiga zabe, za su tsayar da 'yan takararsu ba zai gaza ranar  18 ga watan Augusta na 2022, kamar yadda binciken PUNCH  ya nuna.

Haka kuma sunayen 'yan takarar gwamna a dukkan jam'iyyu za a hannunta su ga hukumar zabe a watan na Augusta.
Shugaban hukumar zabe na kasa Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da cewa zaben shugaban kasa za a gudanar da shi 18 ga Fabarairun 2023, hukumar za ta fitar da jadawalin harkokin zaben bayan kammala zaben Anambra wanda ya gudana a 6 ga watan Nuwamba. 
Akwai yiyuwar a samu sauyin ranar zaben 'yan takara bayan shugaban kasa ya sanya sabuwar dokar zabe da aka yi wa gyaran fuska hannu, an kai wa shugaban kasa dokar wadda ake zaton zai sanyawa hannu kowane lokaci daga yanzu.
A sabuwar dokar an baiwa jam'iyyu damar mika 'yan takararsu ga hukumar zabe daga kwana 60 har zuwa kwana 180 kafin ranar zabe, in shugaban kasa ya sanya hannu hukumar zabe za ta yi jadawali kamar yadda dokar ta tanadar.