YANDA ZA KI HAƊA LEMON FARAR SHINKAFA DA DABINO MAI SHEGEN DAƊI
INGREDIENTS
Farar shinkafa (gwangwani 3)
Dabino (kamar guda biyar ko bakwai)
Kanumfari
Madarar gari(dai-dai buƙata)
Sugar (daidai ɗanɗano)
Riɗi (kantu) for decorating if needed.
PROCEDURE:
Zaki fara gyara shinkafarki ki jiƙa ta after some hours sai ki wanke ta ki niƙa a blender.
Kafin nan zaki jiƙa dabino da kanumfari a ruwa ya yi kamar awa huɗu ko biyar.
Sai ki ɗora tukunyarki a wuta ki juye ƙullin shinkafar a ciki ki dinga juyawa gudun kada ya kame ko ya yi tuwo-tuwo. Idan ya dahu sai ki sauke ki ajiye ya huce sannan ki tace, zaki iya ƙara ruwa idan kinga ya yi kauri sosai.
Bayan kin tace sai ki ɗauko dabinonki ki juye a blender har ruwan ki markaɗa sai ki tace ruwan dabinon a cikin na shinkafar.
Daga nan sai ki dama madararki da ɗan ruwan ɗimi daidai yadda za ta ishe ki sai ki juye a cikin haɗin ki saka sukari dai-dai ɗanɗano.
Zaki iya decorating ɗin shi da riɗi ko duk abin da kika yi ra'ayi ko ki bar shi a haka. Sai ki saka a pridge ya yi sanyi ko ki saka ƙanƙara.
Enjoy it.
RUKY'S BAKERY
managarciya