Farashin Sufurin Jirgin Sama Ya Tashi In Da Ake Biyan Dubu 135 Daga Abuja Zuwa Kano
Farashin sufurin jirgin sama ya kara tashi a Najeriya yayin da fasinjoji ke cigaba da bayyana damurwar su, inda yanzu ake biyan N135,000 daga Abuja zuwa Kano.
Ana biya dubu 120 daga Abuja zuwa Sakkwato sabanin baya da ake biya kasa ga haka duk da a lokacin ana koka tsadar kafin wannan farashin.
Rahoton Aminiya Daily Trust ya bayyana wannan yanayi ya sa mutane da dama na fasa tafiyar su ko kuma su nemi wasu hanyoyin mafi sauki, da suka hada da hanyar mota wadda ita kadai c eke da sauki a kasar, domin tsaro ya karya sufurin jirgin kasa da ya fara zagaya sassan kasar.
Kamfanonin Sufurin jiragen sama dai sun alakantar da tashin gwauron zabon da farashin tikitin jirgin sama yayi ga tsadar mai da sauran harkokin gudanarwa a kamfanonin.
A shekarar baya, ana sayar litar mai kasa da naira N200, yanzu kuma ya haura N800, kuma ana sa ran zai kai naira N1,000 saboda yaki da ake yi tsakanin kasar Rasha da Ukraine.
Tsayar da ayyukan kamfanonin jirgin sama na Aero Contractors da Dana da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kasa (NCAA) yana cikin abun da ya kara tsadar tikitin sufurin jirgin sama a Najeriya.
Bincike ya nuna cewa kusan duka kamfanonin jiragen sama a Najeriya sun kara kudadensu, inda mafi karanci ya fara daga N80,000, a maimakon N50,000 a baya.
managarciya