CREAM CHICKEN SOUP:Hadin Kaza Domin Inganta Lafiyar Jiki

CREAM CHICKEN SOUP:Hadin Kaza Domin Inganta Lafiyar Jiki

BASAKKWACE'Z KITCHEN


     


CREAM CHICKEN SOUP



INGREDIENTS
*kaza
*madara
*corn flour
*gishiri da maggi
*kayan qamshi.

METHOD
Dafarko za ki dafa kaza da dan kayan miya da kayan kamshi ki sanya maggi da gishiri. 

Ruwan dan daidai za ki sa yadda ko bai tsotse ba ya kasance  kadan ne wanda yahau sama. Ki zauna ki zare kasusuwan kazar,  zallan naman kawai ki ka aje a gefe guda. 
Saiki dama corn flour din ki zuba akai, haka ma madarar dama ta za ki tare da corn flour din. Ki maida wannan tsokar kan wuta saiki zuba hadin madarar akai hadi da juyawa a hankali sai ki rufe zuwa minti biyar sai ki duba ki ga idan kina so da kauri ne to idan ba kauri sai ki sanya ruwan zafi ki juya har yayi daidai da bukatarki..
Wannan hadin bayan dan karen dadi da yake da shi yana inganata lafiyar jikin dan adam.
Sannan a duk sanda mace za ta irin wannan hadin ana bukatar ta natsu a lokacin hada shi gudun ka da a yi hasarar abin da aka sawo, in aka yi kuskuren hada shi ba daidai ba zai ciwo ba, in har an dage sai ci kuma ciko na iya biyo gyarte.
Mata 'yan uwana a kula. 

MRS BASAKKWACE