'Yan gari sun kashe 'yan bindiga 6 da kuma kubutar da waɗanda aka yi garkuwa da su a Sakkwato 

'Yan gari sun kashe 'yan bindiga 6 da kuma kubutar da waɗanda aka yi garkuwa da su a Sakkwato 
Mutanen garin Bimasa da ke ƙaramar hukumar Tureta a jihar Sakkwato sun nuna gagarumin jarumta, inda suka fuskanci ‘yan bindiga, suka kubutar da wasu ‘yan uwansu da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan 6.
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa mazauna garin, ba tare da tsoron komai ba, suka bi sawun ‘yan bindigan har cikin dajin da suke buya, suka fafata da su kai tsaye a wani aikin jarumta wanda ya haifar da mutuwar wasu daga cikin maharan.
 Al’ummar garin sun samu nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin harin.
A wani lamari na nuna nasara, mazauna garin sun dawo da ɗaya daga cikin ‘yan bindigan da suka kama zuwa garin, inda aka yi shagulgula na murna da haɗin kai da kuma jarumtarsu.
Shugabannin al’umma sun yaba da jajircewar mutanen, tare da yin kira ga hukumomi da su ƙarfafa tsaron garin matuƙa, saboda tsoron kai hari na ramuwar gayya daga ‘yan bindiga
Shugaban karamar hukumar Tureta Aliyu Tureta ya tabbatar da kai harin na jarumta ya ce an kashe 'yan bindigar shida an kubutar da shanu da mutane da dama, wanda har yanzu ba su kididdige yawansu ba.