ANA BARIN HALAL...: Fita Ta 38

ANA BARIN HALAL...: Fita Ta 38

ANA BARIN HALAL...

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe

Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

Idan kana/kina sha’awar:

_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._

_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._

_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._

_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._

_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t

*Page 38*

*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559


********
Bayan Abba ya gama sauraron su sai yayi murmushi ya gyara zama,  "ALHAMDULILLAHI Naji daɗin wannan batu na ku, don duk inda akace ƴar'uwa ta rasu tou daɗin zama ya kansa a sake neman auren ƴar'uwarta,  duk da ansamu saɓani a tsakanin su har ta kai ga batun saki, tou naji daɗin zuwan ku, don alama ya nuna Habiba ɗiyata bata zalunci ɗanku Aliyu ba a zaman takewar su, don nayi imani da Allah da ace ta zalunce shi ko ta cutar da ku, babu wanda zanga ƙafan shi a ƙofar gidana don neman auren ɗaya daga cikin ƴaƴana,"  gƴaɗa kai kawai iyayen Aliyu sukeyi, Abba ya cigaba bayan yabi kowan su da kallo,  "Habiba, Ayshaa duk abu ɗaya ne yayi su  sannan ƴaƴa nane mafi soyuwa a zuciyana, sanadin halayen su Allah ya saka mun ƙaunar su a zuciyata, yara ne dattawa, masu haƙuri,  yarah ne masu albarka, Allah ya jiƙan habiba",  Abba ya faɗa da wani yanayi a fuskan shi na jimami,
"Kunzo da maganar neman auren ƴar'iwarta, wanda da ko ba ayi zaman lafiya ba Albarkacin wannan jariri zan iya amincewa da buƙatanku, tou amma gaskiya banji daɗin riƙon da Aliyu da ku iyayen shi kukayi wa habiba, tabbas banji daɗi ba, amma komai ya wuce zamuyi zumunci a tsakanin mu ko dan albarkacin wannan jariri, amma maganan aure da Ayshaa abune ba mai yiwuba, don a yanzu akwai maganan aurenta da wani yarona, har an saka rana, kunga kuwa duk dattijon arziki baya magana biyu",  Abba yana kaiwa nan ya miƙa musu hannu suka sake gaisawa, sannan yace su gayawa Aliyu duk lokacin da yaji yazo ko shi ko iyayen shi da ƴan'uwanshi ganin yaro ƙofa a buɗe take, amma maganan bashi ɗa kuma kada ya saka a ranshi, don ya wufantar mun da ƴa da abinda ke cikinta, bai san lafiyan su da komai da suke ciki ba har sai da Allah yayi ikon shi tukun na gan shi gidan nan, bawai na riƙe shi bane a zuciyata, a'a kawai zanyi abun da nake ga shine dai-dai, nagode da zuwanku neman sake haɗa iri dani a karo na biyu".

A kunyace ɗaya daga cikin ƙanin baban su Aliyu ya ɗan risina yana yiwa Abba godiya, sannan dukkansu suka sake bawa Abba haƙurin abunda ya faru, don gaskiya ne sun san basu kyauta ba, lokacin da Aliyu yayi saki babu wanda ya biyo bayan habiba, haka dai suka fita duk jiki a sanyaye, 
Gida suka wuce wurin mummy, bayani dalla -dallah suka mata, gaba ɗaya ran mummy ya ɓaci, a fusace tace,   "tou ae dama tun farko Aliyu baice yana son habiba ba, kuma bamuce habiba tana da aibu ba, kawai naƙita saboda halin mahaifiyar ta ne, don Aliyu ba'a hayyacin shi ya furta ya amince da auren ta ba, kuma lokacin da ya dawo hayyacin shi ya nuna baya sonta, amma ae dana san habiba tana raya baza'a taɓa barin ya auri ayshaa ba ae ban nuna komai ba, amma da habiba ta rasu sai naga akwai dama da Aliyu zai maye gurbin habiba da ƴar'uwarta, wanda dama tun farko itace zaɓin mu da shi baki ɗaya",  cikin ɓacin rai ta ƙarasa maganan, su dai haƙuri suka bata suka tashi suka fice,  cike da ɓacen rai ta ƙira Aliyu ta zayyane mish komai, dama yayi tafiya baya gari,  "mummy wani maganan aure aka tsayarwa Ayshaa da shi? Kawai munafurcin uwar habiba ne ta hana komai, ki ƙira ita ummie kiji komai daga gareta",  sallama sukayi mummy ta ƙira ummie a lokacin, nan dai ummie tayi namijin ƙoƙarin sanarwa mummy akwai maganan aure akaina, wanda zan aura ma cikin satin nan zai gama ya dawo,   "duk da haka dai ummin su a duba al'amarin Aliyu, yana son Ayshaa sosai fah, kuma ashirye yake daya haƙura da wancan maganan auren idan Ayshaa zata amince,"
 Murmushi ummie tayi tace,  "gaskiya koda zai auri ayshaa bazan so a fasa maganan auren shi da yarinyar da ta ke matsayin ƴa a wurinki ba,  ga magana kuma yayi nisa, kawai dai mu ƙara addu'a, Allah ya zaɓa abunda yafi alkhairi a tsakani",  badon mummy taso ba tayi sallama da ummie akan idan Aliyu ya dawo zaizo ya samu ayshaa suyi magana a tsakanin su.

Zuwa dare Abba ya ƙiramu nida ummie zuwa parlon hajiya ummah, achan muka same su harda yayah muhammad, nan Abba ya gaya mana yadda sukayi da iyayen Aliyu,  kuma ya sake jaddada bai hana Aliyu yazo ya ga ɗanshi ba,  amma su yayah muhammad su zama shaidah har abada bazai bashi riƙon yaron habiba ba, dom sakamakon izayan da suka yiwa habiba kenan, nan hajiya ummah ta tafka salati hannu riƙe da bakinta tace,   "amma dai Aliyu da iyayen shi anyi sokayen banza, yoo sokaye mana, ku wahar da habiban don babu kunya a idonku kuzo kuma neman auren ƴar'uwarta? Da shegen baƙar fuska kaman na boss ɗin indian film ya kwaso ƙafa yana zabgegen bazawari yace Ayshaa budurwa wanda zata auri saurayi yake so? Tou haram wannan shirmen ba'a gidan Usmanu na ba, don ko Gwamnah ne mahaifin shi bai isa yaja da kai ba usmanu, nera yafi ka ko suna a gari"?  Dariya ne ya kubcewa yayah muhammad yace,  "ballantana ma besty kam bata son wani Ali black, A.G ɗinta kawai tace sai shi, bawai don farin fuska bako besty"? Ya faɗa yana duba na da murmushi a fuskan shi,  sunkuyar da fuskana nayi ina duban fuskan Sabeer da yake rungume akan cinyata yana bacci,  ido na ƙura mishi ina jin wani irin son shi alokacin kaman zai fasa mun ƙirji na, ummie ce cikin murmushi take zayyana musu yadda sukayi da mummyn Aliyu, nan ma hajiya sake rabka salati tayi tace,  "amma kuwa sun tabbata manyan sokaye, daga uwar har ɗan",  ta maida kallonta kan Abba tace,   "ae wannan satin ne dawowan Aminun ko?"  Abba ya ɗaga mata alaman haka ne,   "tou kayi aniya sati na sama a sambaɗa auren nan",  tayi ƙasa da murya har tana sunkuyowa kaɗan tace,  "gama zafin uwar shinnan da yadda tafi ƙarfin Hauwa da zuriyarta da suka shahara a yawon bin malamai, tou itama bazata gaza bin bokaye ba, tou bokaye mana, don itama ae Hauwan su tabi ta jawo hankalin Aliyun ya bar Ayshaa ya dawo kan nata ƴar,  amma da yake na uwar Aliyun sun fi shahara ae kaga abun baiyi lestin ba, tunin yayi espiya",  ta faɗa tana watsa hannu.

Ɗago kai Abba yayi da sauri ya maida kallon shi kan ummie,  "dama bada amincewar ayshaa ya fara neman habiba ba ne"?
Ita dai ummie bata ce komai ba, sai kallo na da ta ɗanyi ta kawar da kanta gefe,  "dama baka da labari ne? Lallai khadijah kin cika cikakkiyar bafulatana, kawaicinki yakai duk inda ba'a zato, tou Ayshaa ya fara gani a bikin ƴar'uwarshi  Ƙawarsu, ya kware yana sonta, ita kuma marigayiya ban san ya akayi ba, don bana ce taci amanar ƴar'uwarta ba tunda ƙasa ya rufe idanunta, kuma da kunya ga idon ɗanta na faɗi wani mummuna akanta, tou haka dai muka samu zance ya juye ya koma kan habiba,  amma dai ba wai da yardar Ayshaa ba yadda suka tsara maka, juya kanshi akayi ya bar kan Ayshaa, daga wannan rana kuma uwar habiba ta raba tsakanin ayshaa da habiba, Allah dai masani amma shu'umancin uwarta na shige da fice wurin bokayen da baka son afaɗa ne ya tabbatah, shi kuma Aliyu bayan aure Allah ya kuɓutar da shi uwarshi ta tashi tsaye ta lalata ɗan ƙaramin shirkan Hauwa, don daga ganin idon uwar Aliyu gwaska ce, tou komai dai ya karye Aliyu ya dawo hayyacin shi yace baiji ba bai gani ba baya son habiba, don ba ita yace yana so ba, ita kuma marar kunyar ƙanwar tatah Raliya ta tsayar mishi rashin kunya ya labga musu uban na jaki, kaga asalin ƙiyayyan shi da ita marigayiya kenan, sharrin rashin da ce da uwa ta gari".

Abba ido ya zuba mun kaman bazai sake furta komai ba, chan kuma sai yace,  "Aysha ki yafewa ƴar'uwarki, nayi imani ko da laifin habiba tou babbar mai laifin uwartace, don Allah ina roƙon arzikin ki kiyafe mata, taci darajana"!
Hawaye na saka hannu na share,  "Abba ni ban taɓa rike habiba da zuciya ba ɗaya ba, kuma ni tun farko ban so Aliyu ba, shiyasa ma ni banja ba, amma ni ban riketa da komai ba tun farko,  Allah ya jiƙanta da rahma",  na ƙarasa ina share hawayen da bansan ranan daina shi ba.

Addu'a sosi Abba ya mana na alkhari gaba ɗaya ƴaƴan shi , sannan ya umurce ni da na je na cigaba da kula da yaro na, tashi nayi ima rungume da Sabeer na fice, ina ganin hajiya ummah da ummie suna ta share hawayen su.


Ranan friday da 6:00am  jirgin su A.G ya sauƙesu a garin lagos,  9:00am kuma suka tashi zuwa Abujah, amma A.G bai shiga bauchi ba sai ranan saturday da yamma, don basu samu flight me zuwa bauchi ba, dole suka bugu mota sai bauchi, ya iso ya samu gidan a cike, ga Hudah ga Heedayah  da suke ta girke-girke don isowan big broh, twins ɗin ta suna ta shawagi a tsakani, hatta Daddah ranan a gidan ta wuni tare da goggo, suna dakon isowan A.G, suna isowa kuwa su hudah sukaje suka rungume shi suna murnan dawowan shi, ranan dai ya ɗan sake musu har yana zolayan heedayah washi take girkin nan ko dai wa M.G ne?  Rufe ido tayi takasa bashi amsa sai dariya da takeyi, haka dai suka kasance cikin farinciki, mummy kaman ta goya ɗanta, gashi wannan dawowan yayi kyai sosai yayi fari ya ƙara jiki, don har M.G na tsokanan shi ya samu kan Ayshaa ne yasaka ya nutsu bakaman farkon tafiyan shi ba, shidai murmushi kawai yakeyi baice komai ba, anyi sallan ishaa duk suka koma parlor suka zauna, bayan M.G ya mayar da su Goggo da Daddah, ido ya zubawa M.G dayaga ya wani share shi yaƙi kallon shi, ganin bazai kalle shiba ya sa ya aiki heedayah ta bar Parlon, harara M.G ya jefe shi da shi yana gyaɗa kai, alaman zamu haɗu, share shi A.G yayi, sai ya tura mishi text,  "wai me kake nufi ne da bazaka rakani wurin beauty ba"?
Dariya M.G yayi yaƙi maida mishi reply, chan sai A.G ya dubi mummy yace,  "mummy key ɗin motan ki please"?  Ido ta zaro waje tace,  "haba son yau ɗaya kam doug ta mana haƙurinka mana, muna marmarin ganinka ae",  kunya ne yaji ya rufe shi, tun bama da M.G ya kwashe da dariya ba,  "mummy ba wurinta zanje ba fah, phermacy nake son zuwa na duba wani magani",  ya faɗa yana zaro ido, M.G yayi wuf yace,  "Indo pharmacy ba",  dariya dukkan su Parlon suka saka, Shima dariya ƙaryan da yayi ya bashi, haka dai ya daure ya zauna da su har zuwa 9:30pm,  a maraice ya dubi mummy yace,  "zanje na huta mummy",  murmishi tayi tace,  "hakan na da kyau son, jeka huta akwai gajjiyan karatu ae",  bai jira shaƙiyancin da M.G yake mishi ba ya wuce side ɗinsu, da sauri ya rarumo wayan shi ya zabga wa Beautyn shi ƙira.

Dom Allah ayi haƙuri da page ɗin yau, gobe insha Allahu zaifi haka


Ummu khalil akwai bakin magana yau?


*AUNTY NICE*