Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Lakurawa 6 a jihar Sokoto tare da kwato makamai

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Lakurawa 6 a jihar Sokoto tare da kwato makamai

Dakarun hedkwatar tsaro na musamman na Operation Brigade sun gudanar da wani samame na hadin gwiwa kan 'yan ta'addar Lakurawa a karamar hukumar Gudu ta jihar Sokoto.

A cewar wata sanarwa da aka sanyawa hannu tare da mikawa manema labarai a ranar Alhamis ta hannun kodinetan cibiyar hadin gwiwa ta kafafen yada labarai, Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, harin ya kai ga kazamin fadan wuta, inda aka kashe ‘yan ta’adda shida.

Sojojin sun kwato abubuwa kamar haka daga farmakin, bindigogi kirar AK-47 guda hudu, alburusai 160 na musamman 7.62mm da kuma akwati 1 na alburusai 12.7mm.

Sai dai kuma abin takaicin shine an kashe jaruman sojoji biyar da suka sadaukar da rayukansu a yayin da suke gudanar da ayyukan tsaro.

Daga Abbakar Aleeyu Anache