'Yan Bindiga Sun Ƙara Kai Mummunan Hari Ƙauyuka 4 a Sakkwato, Sun Kashe Rayuka Da Dama 

'Yan Bindiga Sun Ƙara Kai Mummunan Hari Ƙauyuka 4 a Sakkwato, Sun Kashe Rayuka Da Dama 

Akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu yayin da wasu gungun ƴan bindiga suka kai farmaki ƙauyuka huɗu a jihar Sakkwato daga ranar Litinin zuwa Talata. 

Ganau sun shaida wa Premium Times cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mazauna kauyukan a hare-haren cikin kwanaki biyu kaɗai. 
 
A cewar mazauna yankin, ƴan bindigan sun kai farmaki kauyen Kajiyo a karamr hukumar Goronyo, Chaco a ƙaramar hukumar Wurno, Lambar Rabah a ƙaramar hukumar Rabah ranar Litinin 
Washe gari kuma maharan suka sake shiga kauyen Rara da ke ƙaramar hukumar Rabah ranar Talata duk a jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yamma. Yadda yan ta'adda suka tafka ɓarna a kuyukan Mazauna sun ce yan bindigan sun kashe mutum huɗu tare da sace wasu 13 a kauyen Kajiyo yayin da suka yi ajalin rayuka uku a kauyen Lambar Rabah. 
Haka nan kuma sun halaka mutum biyu kana suka yi awon gaba da wasu da dama a kauyen Rara, yayin da suka yi garkuwa da jama'a masu yawa a Chaco. 
"Da yawa sun ɗauka zasu sace duk wanda suka haɗu da shi ne kawai amma sai suka shiga gida-gida, garin haka ne suka ɗauki matana guda biyu." 
Mutumin ya bayyana cewa ba ya gida lokacin da yan bindiga suka suka shiga kauyen har suka ɗauki matansa, rahoton Sahara Reporters. 
Wani mazauni na daban, Ibrahim Halilu ya ce dan uwansa Hussaini Bello na cikin wadanda aka yi garkuwa da su a harin wanda ya dauki tsawon sa’o’i. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i, bai amsa kira da sakon da aka aika masa kan sabbin hare-haren ba.