Yadda sabon Bidiyon Waƙar TARKO ke haskawa a masana'antar Kannywood
Daga Ibrahim Hamisu.
Kamfanin Bee Safana production Place ya fito da wani sabon Bidiyon waƙa mai suna TARKO, wanda fitaccen Jarumi a masana'antar Kannywood Daddy Hikima (Abale) da fitacciyar Jaruma mai haskawa Bilkisu Bee Safana suka fito a ciki,
Wakar wacce ta fito da sabon salo mai ban sha'awa ta samu karɓuwa kuma tana kan samu a daidai wannan lokaci. Bidiyon waƙar ya nuna yadda wani azzalumin shugaba ke kama wata budurwa (Bee Safana) ya daddaureta da igiya yayin da shi kuma masoyinta (Abale) ya ke zuwa yana arangama da wadannan mutanen mutane don ganin ya kwato kwato masoyi yar ta, amma duk a cikin waƙe,
Bee Safana hakika ta taka rawar ban mamaki, ganin irin yadda aka daddaureta da igiya a wakar, wanda wannan ba kowace Jaruma ba ce za ta iya hakan,
Babban darakta a Masana'antar Kannywood wanda shi ne Furodusan waƙar Kamilu Ibrahim Dan Hausa ya bayyana cewa abubuwa uku ne suka sanya waƙar farin jini inda ya ce:
"Abu na farko shi ne mun yi amfani da salo wanda ba'a saba gani ba a Kannywood wanda wasu ma da dama gudinsa suke, na biyu mun yi amfani da Jarumai da ake yayi wato Daddy Hikima wato (Abale)da kuma Jurumar wakar Bilkisu Bee Safana da take tashe a yanzu,
"Sai abu na uku shi ne mun samar da mutane 500 da suka fito a wakar, sannan muka samu kwararru da suka gina mana alkarya, inda za'a ga cewa wani Azzalumin shugaba ne ya ke kama karya yake garkuwa da mutane da amfani da miyagun kwayoyi duka dai don masu kallo su Nishadantu to wannan ya sa wakar ta samu karɓuwa a cikin al'umma" a cewa Kamilu DanHausa,
Bidiyon waƙar wanda ya fito a yan kwanakin nan na sabuwar shekarar 2024 za'a iya kallonsa a kafar YouTube da kuma shafin Daddy Hikima Yu tube.
managarciya