Sojojin Nijeriya Sun Kashe 'Yan Bindiga 286

Sojojin Nijeriya Sun Kashe 'Yan Bindiga 286
Daga Nabila Khamis
Hedikwatar tsaro ta kasa (DHQ), ta ce sojojin sun kawar da 'yan ta'adda akalla 286, sun kama wasu 244, tare da kubutar da mutane 122 da aka yi garkuwa da su awurare daban-daban na kasar Nijeriya a cikin makon da ya gabata.
 
Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba, ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayar da karin haske kan ayyukan rundunar a ranar Alhamis a Abuja.
 
Buba ya ce sojojin sun kuma kama wasu mutane 83 da suke satar mai tare da hana barayin man kudaden da aka kiyasta ya kai naira biliyan biyu da miliyan dari biyar a cikin makon da ake tantancewa.
 
Ya kara da cewa sojojin sun kwato makamai iri-iri 587 da alburusai kusan dubu takwas da suka hada da bindigogi kirar AK47 guda 207, bindigogi kirar gida guda 56, bindigogin fafutuka guda 17, da dai sauransu.