Murna Ta Koma Ciki: 'Yan Bindiga Sun Sace Mata Biyar Da Suka Tafi Buki  a Katsina

Murna Ta Koma Ciki: 'Yan Bindiga Sun Sace Mata Biyar Da Suka Tafi Buki  a Katsina

 

Aƙalla mutum huɗu ciki har da dan sanda guda ɗaya ne aka kashe yayin da aka yi awon gaba da wasu da dama a lokacin da ƴan ta'adda suka kai hari a Domawa a ƙaramar hukumar Danmusa ta Jihar Katsina a daren ranar Alhamis. 

An kuma sace wasu ƴan mata biyar da wani mutum ɗaya a wani hari na daban da aka kai Sukola, da ke ƙaramar hukumar Bakori a jihar. 
Jaridar Premium Times ta ambato wata majiya na cewa ƴan ta'addan sun kai hari a cikin ƙauyen na Domawa ne ƴan mintuna kaɗan bayan ƙarfe 9:00 na dare. 
"Ƴan ta'addan sun shiga cikin ƙauyen inda suka fara harbi ba kakkautawa domin tsoratar da mutane. 
Mutum ukun da ƴan ta'addan suka kashe, ƴan ta'addan sun ɗauke su a matsayin barazana, domin a lokacin da (ƴan ta’addan) suka ce su bi su, sai suka ƙi." 
Ya bayyana sunayen waɗanda aka kashe a matsayin Sa’idu Mai Kyaran, Na Doguwa da Suyudi Mai Tabarma yayin ya ce sunan ɗan sandan Hassan.
A yankin kudancin jihar Katsina, ƴan ta'addan sun kai wani hari da ya kai ga yin garkuwa da wasu ƴan mata biyar da suke halartar wani bikin ɗaurin aure a ƙauyen Sukola.
Wani shugaban matasa a ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa "Su (ƴan matan) sun fito ne daga ƙauyuka daban-daban da ke kewayen Sukola. 
Sun je kauye ne domin taya murna ga wata ƙawarsu da za a yi bikinta a ranar Asabar. 
Kun san mata suna da shagulgulan da suke kafin ɗaurin aure, bayan an tashi shagalin dare ne ƴan ta'adda suka far wa ƙauyen." 
Ya bayyana sunayen ƴan matan da aka sace matsayin Maryam Sani, Maijidda Kabir, Abida Matthew da Maryam Ibrahim. 
Ya ce bai san sunan ta ƙarshen su ba. A yayin harin da aka kai da misalin ƙarfe 11:00 na dare, majiyar ya ce ƴan ta'addan sun zo ne da “makamai da dama,” inda suka toshe duk wata hanyar shiga cikin ƙauyen tare da cigaba da harbe-harbe domin haifar da ruɗani. 
Legit Hausa ta tuntubi muƙaddashin kakakin rundunar ƴan sanda jihar Katsina, Abubakar Sadiq, domin samun ƙarin bayani kan ƙoƙarin da ake wajen ceto ƴan matan, bai dawo da saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.