Tsohon mijin Diezani ya kai ta ƙara don haramta mata amfani da sunansa
Tsohon babban hafsan sojin ruwa a Najeriya, Rear Admiral Alison ya kai ƙara gaban kotu domin hana tsohuwar mai ɗakinsa Diezani Alison Madueke yin amfani da sunansa.
Madueke ya buƙaci kotu ta bai wa tsohuwar ministan man fetur ɗin umarnin ta koma yin amfani da sunan mahaifinta Agama kasancewar aurensu ya mutu.
Ya kuma wallafa a jaridun Najeriya da waɗanda ke Burtaniya inda yake neman tsohuwar matar tasa ta daina amfani da sunansa.
A takardar ƙorafin, Madueke ya ce ci gaba da amfani da sunansa haɗari ne ta fuskar shari'a da kuma sha'anin kuɗi musamman yadda take fuskantar shari'a kan aikata laifi a Najeriya da Burtaniya.
Madueke ya ƙara da cewa tsohuwar matar tasa na kunyatar da shi ganin yadda take ci gaba da bayyana kanta a matsayin mai ɗakinsa duk da cewa sun rabu.
managarciya