Dan Majalisa Zai Tallafawa Marasa Lafiya 3000 A Kaduna
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Sabon Gari ta Jihar Kaduna Sadia Ango Abdullahi ya kaddamar da kula da lafiya ga al'umar mazabarsa.
Sadiq ya ce mutane da ke fama da cututtuka fiye da 3000 ake saran za su amfana da wannan shirin.
Dan Majalisar ya bayyana cewa wannan aiki da aka fara yana daga cikin shirin da Tsohon Dan Majalisa Garba Datti Babawo ya tsara na 2023 amma Allah bai nufa shi zai aiwatarba.
Ya ce duk wani aiki da Babawo ko Sadiq suka gudanar sun yi sune domin al'ummar karamar hukumar Sabon Gari.
Sadiq Ango ya ce wannan somin tabi ne duk da cewa watanni uku kachal ya yi a majalisa a matsayin wakili.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Ma'ajin Jam'iyyar PDP na Jihar Kaduna Kasimu Lawal Abbasco ya bayyana Sadiq a matsayin wadda ya kama hanyar fidda Jam'iyyar PDP kunya saboda tsare tsaren da ya far a gudanarwa.
Ya tabbatarwa al'ummar Sabon Gari da cewa aiki yanzu aka fara kuma ba zasu bada kunya ba.
Bikin kaddamarwar ya sami halartar masy ruwa da tsaki na Jam'iyyar PDP da ke yankin da kuma Hakiman Basawa da Sabon Gari.
managarciya