Tinubu Ya Naɗa Mai Magana Da Yawunsa

Tinubu Ya Naɗa Mai Magana Da Yawunsa

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya yi nadin farko a matsayinsa na babban kwamandan rundunar sojin tarayyar Nijeriya.

Inda ya nada, Ambasada Kunle Adeleke, a matsayin babban jami’i mai karbar baki na shugaban kasa (Chief Protocol).


Ya kuma nada tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Legas, Dele Alake a matsayin mai magana da yawun shugaban kasa da Olusegun Dada mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai na zamani.