Duk Wanda Ya Sare Itace Ba Bisa Ka’ida Ba Zai Hadu Da Fushin Gwamnati---Kwamishinan Muhali A Neja

Duk Wanda Ya Sare Itace Ba Bisa Ka’ida Ba Zai Hadu Da Fushin Gwamnati---Kwamishinan Muhali A Neja

 

Daga Awwal Umar Kontagora, Minna

 

 

Gwamnatin Neja ta jaddada dokar hana saran itatuwa a jihar, Kwamishinan muhalli da gandun daji, Injiniya Daniel Habila Galadima ne ya bayyana hakan ga manema labarai littinin din makon nan a Minna.

Injiniya Daniel yace maganar sarar itace a jihar nan haramtacce ne, idan an samu mutum da laifin sarar itace ba tare da izinin gwamnati ba zai fuskanci hukuncin tarar dubu dari ko tarar da dauri.

Domin sarar itace ba bisa ka'ida ba yana daga cikin abinda ke kawo zaizayar kasa, kuma hadari ga cigaban kasa. Saboda mun kafa kotu tafi da gidan ka duk wanda aka samu da laifin yankan itace dan yin katako ko gawayi ba zai tsallake hukuncin kotu ba.

Da ya juya kan bola da ya mamaye manyan garuruwan jihar kuwa, yace maganar kwasar bola ba aiki ba ne da ya rataya a wuyan gwamnati ba, amma saboda hadarin da ke tattare da lafiya da rayukan al'ummar jihar, yasa gwamnati ta rungumi tsaftar muhalli.

Yanziu haka gwamma Abubakar Sani Bello ya  bada umurnin sayo sabbin motoci na zamani da zasu rika kwasar bola a cikin garin Minna.

Mun dan samu tsaiko saboda yan kwangilar da gwamnati ta baiwa aikin kwasar bolan tsadar man dizul yasa ba sa iya aikin kamar yadda ake bukata.

Hakan ba zai sanya gwamnatin tai kasa a guiwa ba, za mu tabbatar mun cigaba da yin aikin yadda ya dace dan kaucewa yaduwar cututtuka a cikin al'ummar jiha ganin yadda mu ke jin labaran yaduwar cututtukan cizon sauro, da wasu cututtuka masu saurin yaduwa da samar da tsaron jiha.