Harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna: 'Yan ta'adda sun saki Shugaban Bankin Manoma

Harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna: 'Yan ta'adda sun saki Shugaban Bankin Manoma
 

Manajan Darakta na Bankin Noma, Alwan Ali Hassan, ya shaƙi iskar 'yanci daga hannun 'yan ta'addan da su ka tashi bam a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

 
A yayin harin ne kuma yan ta'addan su ka yi awon-gaba da wasu fasinjoji, ciki har da shi Hassan ɗin.
 
Wani ɗan uwan Manajan-Darakta ɗin ne ya shaida wa jaridar DAILY NIGERIAN cewa an sako shi a yau Laraba.
Sai dai ba su bayar da wani bayan kan sakin nasa ba waton kudin fansar da aka biya kafin sakin nasa, domin mafiyawan maharan ba su saki mutum haka kawai sai an biya kudin fansa ko kuma ya gudu daga hannunsu.
 
Ya kuma ce an biya kuɗin fansa masu yawa, amma bai fadi takameme ko nawa a ka biya ba.