An daure Hakimi a Sokoto shekara biyar bisa samunsa da laifin safarar miyagun kwayoyi

An daure Hakimi a Sokoto shekara biyar bisa samunsa da laifin safarar miyagun kwayoyi

Babbar Kotun Tarayya da ke Sakkwato, karkashin Mai Shari’a Ahmad Mahmud, ta yanke wa wani hakimi, Alhaji Umar Mohammed (aka Dan Bala) hukuncin daurin shekara biyar da rabi a gidan yari bisa zarge-zarge hudu da suka hada da mallaka da kuma sayar da tabar wiwi kilo 436.38 da kuma  7kgs magungunan sa maye da hukumar NDLEA ta gurfanar da shi a Oktoban 2022.
 An yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu akan kowane tuhume-tuhume na 1 da 2 tare da zabin tarar Naira miliyan 1, da kuma wata takwas akan kowanne, yahin da na 3 da 4 ba tare da zabin tara ba. PM News ta rahoto.
 Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi.