'Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 81 cikin kwana daya  a Sakkwato---Honarabul Aminu Boza

'Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 81 cikin kwana daya  a Sakkwato---Honarabul Aminu Boza

 

'Yan bindiga dauke da miyagun makamai sun yi garkuwa da mutane cikin kwana biyu   a kauyukkan Katuma da Dan Aduwa 15 da Unguwar lalle 10  da Marna 10 da Tsamaye 25 dukkansu a karamar hukumar Sabon Birni dake jihar Sakkwato.

Wata Majiya a Sabon Birni  ta shedawa Aminiya cewa 'yan bindigar da yawansu bai kai 20 ba, sun shiga kauyukkan ne da safen Lahadi suka tafi da mutum 40 bayan sun fita gona domin aikin damina, bayan nan sun sake dawowa a Litinin suka tafi da mutane 20 domin sun fita aikin gona ba da izininsu ba.
Majiyar ta ce 'yan bindigar sun sake tare hanyar Kwanar Maharba da ta hada garin Sabon Birni da Sakkwato in da suka hana shiga ko fita a yankin.

"a kauyen Dan Gawo an harbe mutum 9 biyu sun mutum shida na kwance a babbar asibitin Sabon Birni, kafin su yi garkuwa da mutanen ne suka yi haka, lamarin nan barazanar tsaro ya dawo mana a yankinmu", a cewar majiyar.

Honarabul Aminu Almustafa wanda aka fi sani da Boza dake wakiltar Sabon Birni ta yamma a majalisar dokokin jiha ya ce 'yan bindigar suna addabarsu a wannan Litinin maharan sun shigo sun tafi da mutum 81 a Sabon Birni don kawai sun tafi gona.
"bayan 'yan bindigar sun shigo kauyukkan mu mun kira jami'an tsaro domin ba mu dauki har yanzu da muke magana da kai ba wanda ya zo wajenmu a cikinsu, yakamata gwamnati ta taimaka mana a yankinmu musamman a wannan lokacin da muke ciki na damana," a cewar Aminu Boza.
Ya ce maharan sun harbe mutum 9 biyu sun rasu yayinda sauran ke kwance asibiti.
Jami'in huldar da jama'a na 'yan sandan Sakkwato DSP Sanusi Abubakar duk yunkurin jin ta bakinsa kan lamarin ya ci tura.