Tinubu ya dukufa ne wajen ƙwato kuɗaɗen da aka sace a gwamnatocin baya -- Sarkin Minna

Tinubu ya dukufa ne wajen ƙwato kuɗaɗen da aka sace a gwamnatocin baya -- Sarkin Minna

Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi bakin ƙoƙarinsa wajen ƙwato kuɗaɗen da aka sace a gwamnatocin baya, amma ƴan Najeriya ba su gane ba.

BBC Hausa ta rawaito cewa Sarkin ya bayyana hakan a taron wayar da kan ƴan ƙasa a kan tallafin da Gwamnatin Tarayya ke yi a jihohin ƙasar, wanda ofishin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma ya shirya a Minna na Jihar Neja.

Sarkin wanda Hadinin Minna, Alhaji Maukudi Achaza ya wakilta, ya ce Tinubu na bakin ƙoƙarinsa wajen magance matsalar cin hancin da rashawar da aka yi a baya.

Ya ce tallafin da gwamnatin Tinubu ke yi, yawancin ƴan ƙasar ba su sani ba saboda masu magana da yawun gwamnatin ba sa yaɗa ayyukan yadda ya kamata musamman wajen yin magana da harshen da mutanen ke ji.

"An sace maƙudan kuɗaɗe da dama a gwamnatocin baya, wanda gwamnatin yanzu ke ƙoƙarin ƙwatowa, amma mutane da dama ba su fahimta ba. Sannan tun bayan janye tallafin man fetur, an gudanar da abubuwa da dama domin rage raɗaɗin da ƴan ƙasa suka shiga. Yana da kyau gwamnati ta riƙa wayar da kan mutane a kan shirye-shiryenta a harshen da suke ji," in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.