Mai Baiwa Gwamnan Sakkwato Shawara Na Musamman ya ajiye aiki

Mai Baiwa Gwamnan Sakkwato Shawara Na Musamman ya ajiye aiki

Mai Baiwa Gwamnan Sakkwato Shawara Na Musamman ya ajiye aiki

MAI BAIWA GWAMNAN JAHAR SOKOTO SHAWARA A BANGAREN MASU LALURA TA MUSAMMAN HON. ALIYU UMAR (UBANDOMAN RABAH)YA AJE MUKAMINSA NA ( S A).
Bayaga dogon nazari tare da hadinkai na Magoya Baya a Sokoto da Karamar Hukumar Mulkin Rabah In da mai baiwa gwamnan shawara ya fito ya sanar da su ya ajiye muƙamin saboda haɗin kan jama'a da aka samu wuri daya suka cilasta a ajiye aikin.
A jawabin nasa tsohon mai baiwa gwamnan shawara yace yana tare da sanata Ibrahim Lamido bisa kudirinsa na ciyarda yankin Gabascin Sokoto gaba dakuma kokarinsa na inganta rayuwar talakawan yankin.
Daga karshe tsohon mai bada shawar Yayi godiya ga Allah yakuma kara Godiya ga Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu bisa Aikin da Suka yi na tsawon Shekara Daya.