Shugaban Kamfanin Motalba Solid ya yi wa Gwamna Raɗɗa ta'aziya kan rasuwar mahaifiyarsa 

Shugaban Kamfanin Motalba Solid ya yi wa Gwamna Raɗɗa ta'aziya kan rasuwar mahaifiyarsa 

Shugaban Kamfanin Motalba Solid Ltd Kaduna ya yi wa Gwamnan Katsina Dakta Umar Dikko Raɗɗa ta'aziya kan rasuwar mahaifiyarsa da aka yi yau Lahadi bayan jinya da ta yi.

Alhaji Mohammad Adamu Aliero ll (Talban Aliero)
 yana Mika Sakon ta'aziyyarsa ga Iyalan  Umar Radda bisa Rasuwar Hajiya Safara'u Umaru Baribari, Mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Radda wadda Allah yayiwa Rasuwa.

"Amadadin Kamfani da iyalai muna miƙa saƙon ta'aziyar mu, Allah kajikan ta da rahama, ya baiwa dangi da masoya haƙurin jure rashinta, Ameen."

Talba ya ce wannan rashi ne ba ga dangi kawai ba, ga Katsina da Arewa da Nijeriya gaba ɗaya an rasa mace mai hakuri da taimakon al'umma ga son zumunci.