Gwamnan Wike  Ya Baiwa Sakkwato Da Wasu  Jihohi 4 Gudumuwar Naira Biliyan 2 

Gwamnan Wike  Ya Baiwa Sakkwato Da Wasu  Jihohi 4 Gudumuwar Naira Biliyan 2 

 

Mai girma Gwamna Nyesom Wike mai mulkin jihar Ribas ya saba taimakawa jihohi da daidaikun mutane da-dama da tallafin kudi. 

Mun fahimci a watanni 15 da suka wuce, gwamnan na Ribas ya bada gudumuwar Naira biliyan 2.1 ga jihohin da bukata ta taso masu a fadin kasar nan. 
Punch ta bi yadda gwamnan ya raba gudumuwa daga watan Junairun 2021 zuwa Oktoban nan. 
1. Jihar Sokoto A lokacin da gobara ta ci babbar kasuwar Sokoto, Gwamnan Ribas ya tallafawa Gwamna Aminu Tambuwal da kyautar N500m a ranar 10 ga Junairun 2021. 
Gwamna Atiku Bagudu mai makwabtaka da Sokoto, ya ba ‘yan kasuwar gudumuwar N30m a lokacin.
2. Jihar Akwa Ibom Nyesom Wike ya bada kyautar N600m ga jihar Akwa Ibom a Mayun 2021. 
Gwamnan ya bada kudi wajen gina asibitin koyar da likitoci da ke Awa a garin Onna. 
3. Jihar Bayelsa Kokarin gwamnan bai tsaya nan ba, ya bada N500m domin a gina jami’ar aikin likitanci a garin Yenagoa.
 An yi wannan a watan Fubrairun shekarar nan. 
4. Jihar Kaduna Da Gwamnan ya zo Kaduna domin yakin neman zama ‘dan takaran PDP a 2023, ya bada gudumuwar N200m domin kula da wadanda rikicin ‘yan bindiga ya ci. 
5. Jihar Legas A makon jiya Nyesom Wike ya ziyarci Legas, nan ma ya raba N300m ga matan jami’an gwamnatin Legas, yace ya yi hakan domin yabawa ayyukan da ake yi.