Gwamnatin Zamfara za ta Gina tashoshin mota na zamani don samar da aikin yi ga mutum 5000 

Gwamnatin Zamfara za ta Gina tashoshin mota na zamani don samar da aikin yi ga mutum 5000 
Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya karbi bakuncin kungiyar sufuri ta kasa reshen jihar Zamfara(NARTO) da ta masu dakon man fetur(PTD) a Gidan gwamnatin jiha dake Gusau ranar Talata data gabata.
Haduwar an tattauna muhimman abubuwa da suka shafi kungiyoyin da jihar Zamfara har da batun samar da tashoshin zamani a babban birnin jiha.
Gwamnan Lawal ya bayyana kudirinsa na samar da tashoshin ne domin rage cinkoson ababen hawa a jihar a kokarinsa na zamanantar da jihar.
Gwamnan ya kara da cewar ya tsara samar da tashoshin mota biyu a hanyoyin fita daga cikin Gusau don bunkasa sufuri, hakan zai taimaki karkon hanyoyin da ake da su a jiha.
Da yake yiwa kungiyoyin biyu jawabi ya ce "na bayar da umarnin gina tashar mota tirela kan hanyoyi biyu na shigowa cikin Gusau, dayan ta Funtuwa zuwa Gusau, da Gusau zuwa Sakkwato, ina gayyatar kungiyar NARTO da  PTD su shiga cikin kwamitin aikin a wuraren nan.
“Za a natsu sosai a samu wuri Mai kyau da zai yi daidai da Tirela da dukkan bukatun da suka zagaye aikin ba kawai don a samar da kudin shiga a jiha ba, har da samar da gamsuwa ga bakin da za su shigo," a cewar Gwamna.
Shugaban kungiyar NARTO Alhaji Mustafa Musa ya baiwa Gwamna tabbacin za su ba da goyon baya kan lamarin.
Ya ce "kungiyoyinmu biyu suna tare da gwamnati a wannan kudiri na samar da tashar Tirela, mun yi farinciki da aka gayyace mu shiga cikin aikin za mu ba da hadin Kai a tabbatar da an kammala aikin, wannan tashoshin za  su samar da aikin yi ga mutanen Zamfara sama da 5000 ba za mu yi wasa da aikin ba," kalaman Alhaji Musa