Miji Ya Watsawa Matarsa Tafasasshen Ruwan Zafi Tana Barcin Dare

Miji Ya Watsawa Matarsa Tafasasshen Ruwan Zafi Tana Barcin Dare

Magidanci Isaaq Ekeh ya watsawa matarsa Stella Ekeh tafasasshen ruwan zafi tana tsaka da barcin dare abin da ya kawo mata samun matsala a jikinta gaba daya. 

Kamfani Dilancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa lamarin ya faru ne ranar 31 ga watan Mayun 2022 da misalin karfe 3:00 na dare a unguwar Alakija da ke Karamar Hukumar Amuwo-Odofin da ke Jihar Legas.

Matar tasa dai ta kone sosai har fatar ta sabule, kuma ta sanar da manema labarai ta wayar tarho cewa, lamarin ya faru ne bayan sun kamala cin abincin dare da sauran ‘ya’yansu hudu, kafin  daga bisani su je su kwanta.

Stella ta ce: “Wajen karfe 3:00 na dare ina tsaka da barci a dakinmu da shi, kawai sai ji na yi ya sheka min tafasasshen ruwa”.

“A gigice na farka ina ihu, abin da ya taso ‘ya’yannmu da ke barci ke nan, inda suka shigo suka ga fatata na sabulewa. Nan take suka wuce da ni asubitin kashi na Igbobi aka kwantar da ni domin ba ni kulawa”, inji ta.

Ta ci gaba da cewa “Abin da ke ba ni mamaki shi ne ba fada muka yi ba, ko wani musu ballantana na ce shi ne dalilin da ya sanya ya min wannan ta’asar domin huce takaici”.

Kazalika ta ce yanzu haka mijin nata ya koma kauyensu da ke Jihar imo, bayan aikata ta’asar.

A nasa bangaren kakakin Rundunar ‘Yan Sansan Jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce ba shi da labarin aukuwar lamarin, saboda babu wani rahoto da aka kawo ofishinsu, don haka ya shawarci matar da ta garzaya ofishin ‘yan sanda mafi kusa domin daukar matakin da ya dace akan mijin nata.