Sanata Adamu ya sanar da Ahmed Lawan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na maslaha
Rahotanni da ke fitowa da ga Abuja a yanzu sun bayyana cewa Shugaban Jam'iyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sanar da Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na maslaha a jam'iyar.
Adamu ya bayyana hakan ne a taron gaggawa na Kwamitin Ƙoli na jam'iyar, NWC a yau Litinin a Abuja.
Sai dai kuma Adamu ya ce sauran ƴan takara irin su Asiwaju Bola Tinubu; Yemi Osinbajo; Kayode Fayemi da David Umahi za su iya shiga zaɓen fidda-gwani da za a yi gobe a Eagle Square, Abuja.
managarciya