Kwamishinan Tambuwal  Ya Fadi Gwamnatin Da Ke Da Alhakin Gyara Rawun Mai Ruwa

Kwamishinan Tambuwal  Ya Fadi Gwamnatin Da Ke Da Alhakin Gyara Rawun Mai Ruwa
 
 

"Shi Round About  yana kan titin da ake kira Trunk A, watau mallakar Gwamnatin Tarayya. Su ke da alhakin gyaran shi idan ya sami matsala. Amma saboda kulawa da lafiyar Al'umma, da jin dadin su, sau da yawa Gwamnatin Jihar Sokoto takan rufe ido, ta gyara shi, da ire - iren su idan suka lalace; duk da yake ba hakkin ta ba ne,"kalaman Bashir Gidado Kwamishina a gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal.

 
Haka ma ya ci gaba da cewa a turakarsa ta facebook "Idan kuna tunawa, bara ma Gwamnatin Jihar Sokoto,  ta gyara wannan Shatale - talen, da wasu a cikin Birnin Sakkwato. Kuma kwanan bawa kadan, Hukumar gyaran titunan Gwamnatin Tarayya (FERMA) tayi gyaran titin dake kusa da wannan round about din, amma abin mamaki, sai suka tsallake shi basu gyara ba.
 
"Yanzu haka, Hukumar tsara birane ta Jiha (SURPB), na dab da daukar mataki na wuccen gadi, kafin warware matsalar na dindindin. 
 
"Kuma muna magana da wani kamfani mai zaman kan shi, akan su dauki nauyin gyara wannan Shatale - tale, a matsayin tasu gudummuwa, ga ci gaban Jihar Sokoto" kalamansa da yake ganin sun dace a yi wa jama'a bayani.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa tare da wasu mutane masu tausayin al'umma kan halin da wurin ya shiga sun hada karfi sun yi gyaran wucin-gadi don samar da sauki ga ababen hawa.