'Yan Bindiga Sun Harbe Lauya A  Zamfara

'Yan Bindiga Sun Harbe Lauya A  Zamfara
 

Rundunar ‘yan sanda a  jihar Zamfara, a yau Juma’a ta tabbatar da kisan wani mamba a ƙungiyar lauyoyin Najeriya, NBA, Benedict Torngee Azza da wasu ‘yan bindiga suka yi a jiya Alhamis.

 
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ne ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya kisan lauyan a Gusau a yay Juma’a.
 
Shehu ya ce jami’an tsaro na sirri na kan bin sawun wadanda suka yi kisan, yayin da rundunar ta kara karfafa tsaro a yankin da lamarin ya faru.
 
Tun da farko, Shugaban NBA na jihar, Junaidu Abubakar ya ce an harbe  Azza ne bayan ya tsere daga gidansa da misalin karfe 10 na dare.
 
Ya ce jami’an hukumar FRSC da ƴan sanda ne suka ɗauke gawar mamacin zuwa asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau.
 
A cewarsa, makwabta sun shaida masa cewa wasu ‘yan bindiga biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka zo a kan babur ne suka harbe marigayin.
 
“Bayanan sun nuna cewa ‘yan bindigar sun so yin garkuwa da shi ne a gidansa da ke Unguwar Saminaka, bayan shelkwatar FRSC da ke Gusau.
 
“Amma sai ya tsere, ya tuka motarsa ​​da gudu ya nufi bakin hanya. ‘Yan bindigar sun bi shi inda suka harbe shi a kan hanyar wucewa,” ya kara da cewa.
 
Shugaban NBA ya kara da cewa daga baya makwabta sun ji karar harbe-harbe da kuma karar haɗarin mota.
 
“Lokacin da suka fito suka garzaya wurin da lamarin ya faru, sai suka ga Azza ya bude kofar motarsa, ya fito ya nufi bakin titin inda ya zauna, sai jini ya rika zuba da ga nan sai ya ce ga garinku nan.
 
Azza ya fito daga Benue kuma shi ne Babban Associates Benedict Torngee Aza da Associates lauyoyi a Gusau.