Buni ya ƙaddamar da ginin haryar Ngalda zuwa Mutai, Makarantar Mega a Potiskum

Buni ya ƙaddamar da ginin haryar Ngalda zuwa Mutai, Makarantar Mega a Potiskum

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a ranar Alhamis ya kaddamar da fara ayyukan ginin hanyar Ngalda zuwa Mutai mai tsawon 54km, Makarantar Sakandire Mega a Potiskum da ke jihar Yobe.

Gwamna Buni ya bayyana cewa a kashin farko na aikin hanyar ya faro ne daga Gujba zuwa Ngalda, domin sada garuruwan da suke tsakanin Gujba zuwa Mutai, wanda kungiyar Multi-Sectoral Crisis Recovery Project (MCRP) ta aiwatar.

Inda ya kara da cewa a kashi na biyu na aikin wanda ya shafi Ngalda zuwa Mutai, aiki ne wanda Hukumar Sake Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) za ta gudanar da shi.

Ya ce, “Ko shakka babu gina wannan hanyar zai taimaka wajen bunkasa harkokin tattalin arziki ta hanayar safarar albarkatun noma da saukaka zirga-zirgar al'ummar jihar Yobe da kasa baki daya."

"Har wala yau, wannan ita ma wannan Makarantar Mega za ta taimaka wajen rage cunkoson dalibai wanda ya yi yawa a garin Potiskum da sauran sassan wannan jihar." In ji Gwmna Buni.

Gwamna Buni ya yaba wa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari wajen kirkiro da Hukumar Sake Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), haka kuma ya yaba wa shugabanin hukumar bisa jajircewa a ayyukan da suka rataya a wuyansu don sake farfado da yankunan da matsalar tsaro ta shafa a Arewa Maso Gabas. 

A nashi bangaren, Shugaban Hukumar NEDC (MD), Alhaji Muhammed Alkali, ya bayyana cewa hukumar ta yanke shawarar shimfida wannan muhimmiyar hanya tare da gina Makarantar Sakandire ta Mega guda uku a jihar Yobe hadi da sauran yankuna 18 Arewa maso Gabas. 

A cewar hukumar, kowace makaranta za ta kunshi ajujuwa 12, dakin gwaje-gwaje na sashen firamare da sakandare, dakin taron da cibiyar sadarwa ta zamani (ICT).

Sauran muhimman bangarorin da za a gina a makarantun sun hada da sashen gudanarwa, dakin shan magani, rijiyar burtsatse, da injin bayar da hasken lantarki mai karfin 200kva don tabbatar da aiki cikin sauki da tsayayyen wutar lantarki.

Alkali ya ce gina hanyar Ngalda zuwa Mutai mai tsawon kilomita 54 za ta hada al'ummar kananan hukumomin Fika da Gujba, inda ya bayar da tabbacin kammala aikin cikin lokaci. Kana ya ce aikin ginin hanyar zai lakume naira biliyan 12.5.