Tambuwal Ya Rasa Kwamishinansa Na Harkokin Addini

Tambuwal Ya Rasa Kwamishinansa Na Harkokin Addini

 

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya rasa kwamishinansa na ma'aikatar harkokin addinin musulunci Alhaji Usman Suleiman Danmadamin Isa bayan wata gajeruwar rashin lafiya.

Margayin ya bar duniya a yau Jumu'a  yana da shekarru 69 tare da mata hudu da 'ya'ya  25 da 'yan uwa da dangi.
Gwamna Tambuwal ya yi ta'aziyar rasuwar matgayin a wani sako da kwamishinan yada labarai na jiha Alhaji Akibu Dalhatu ya fitar amadadin gwamnati.
Tambuwal ya bayyana margayin mutum ne mai kwazon aiki da sanin yakamata ya roki Allah ya gafarta masa kurakuransa.